Yara 9 Daga Cikin 102 da Aka Sace a Jihar Arewa Sun Samu Nasarar Kubucewa, Bayanai Sun Fito

Yara 9 Daga Cikin 102 da Aka Sace a Jihar Arewa Sun Samu Nasarar Kubucewa, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yara tara daga cikin 102 da aka sace a farkon watan Maris sun kubuta daga hannun mahara
  • Shugaban SEMA a jihar ya ce sun samu labarin cewa yaran tara sun samu hanyar dawowa zuwa sansanin ‘yan gudun hijira
  • Sai dai rahoton sace yaran ya jawo kace-nace inda gwamnatin jihar ta musanta labarin cewa sace yaran aka yi a cikin daji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno – Yara tara daga cikin 102 da kungiyar Boko Haram suka sace sun kubuta daga hannun ‘yan ta’adda a jihar Borno.

Yaran na daga cikin wadanda ke sansanin gudun hijira da aka sace a ranar 4 ga watan Maris yayin da suke diban itace a cikin daji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 4 a jihar Imo

Yaran sansanin gudun hijira 9 sun tsare daga hannun 'yan ta'adda
Rahotanni sun tabbatar da cewa yaran 9 sun samu nasarar dawowa gida. Hoto: Babagana Umara Zulum.
Asali: Twitter

Cece-kuce da aka yi kan sace yaran

Rahotanni sun tattaro cewa ba a ji wata magana ta neman kudin fansa ba daga maharan inda gwamnatin ta tsaya cewa yaran rasa hanyar dawowa suka yi ba sace su aka yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa an yi ta cece-kuce bayan sace yaran inda gwamnatin jihar ta yi watsi da cewa an sace su.

Majalisar Dinkin Duniya har ila yau, ta yi Allah wadai da sace kusan 200 daga sansanin gudun hijira a Borno, cewar NewsNow.

“Gaskiya ba mu yarda an sace yaran ba kawai dai sun rasa hanyar dawowa gida ne, idan da an sace su da zuwa yanzu maharan da sun kira domin neman kudin fansa amma ba su yi ba.”

- Shugaban NEMA, Barkindo Saidu

Martanin shugaban SEMA a jihar

Kara karanta wannan

Budurwa ta siya katon gida a turai tana da shekaru 22, ta yi murnar zama mai gidan kanta

Barkindo ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Ngala bayan rahoton sace yaran a ranar 8 ga watan Maris, cewar Tori News.

"Mun samu labarin cewa tara daga cikin yaran sansanin gudun hijira sun samu nasarar dawowa gida a ranar Juma'a 8 ga watan Maris."
"Bamu yadda da yawan yaran da ake yadawa an sacce ba, mu muka san yawan 'yan sansanin gudun hijirar."

- Barkindo Saidu

Mahara sun sace yaran sansanin gudun hijira

Kun ji cewa 'Yan ta'addan Boko Haram sun sace yara mata 'yan gudun hijira har 319 a jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mata da cewa an sace 'yan gudun hijiran ne a garin Ngala, hedikwatar karamar hukumar Gambarou Ngala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel