InnalilLahi: Tsohon Sanatan PDP, Sodangi Ya Rasu a Daren Farkon watan Ramadan

InnalilLahi: Tsohon Sanatan PDP, Sodangi Ya Rasu a Daren Farkon watan Ramadan

  • Tsohon sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, Abubakar Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya Lahadi
  • Marigayin wanda ya wakilci yankin har tsawon shekaru 12 ya rasu ne a jiya Lahadi 10 ga watan Maris ya na da shekaru 70 a duniya
  • Kafin rasuwar marigayin, shi ne shugaban kwamitin kamfe na Gwamna Abdullahi Sule a zaben da aka gudanar a shekarar 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa – An shiga jimami bayan rasuwar Sanata Abubakar Danso Sodangi ya na da shekaru 70 da haihuwa.

Marigayin wanda ya wakilci Nasarawa ta Yamma fiye da shekaru 12 ya rasu ne a jiya Lahadi 10 ga watan Maris, cewar Nasarawa Mirror.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan APC a Arewa zai biya ma'aikata rabin albashi domin yin azumi cikin walwala

An tafka babban rashin bayan rasuwar Sanata Sodangi a daren jiya Lahadi
Marigayi Sanata bubakar Sodangi ya rasu ne a daren jiya Lahadi. Hoto: Senator Abubakar Sodangi.
Asali: Facebook

Hidimar da Sanatan ya yi wa addini

Har ila yau, marigayin kafin rasuwarsa shi ne ya rike shugaban kwamitin kamfe na Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba mu samu musabbabin mutuwar sanatan ba.

Marigayin ya kuma yi wa addinin Musulunci hidima sosai inda ya kasance cikin kwamitin amintattu na ‘yan agajin Kungiyar JIBWIS a jihar Nasarawa.

Jigon jam'iyyar APC ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da dorewar mulkin jam'iyyar a jihar.

Tarihin rayuwar Sanatan da siyasarsa

An haifi marigayi ne a ranar 31 ga watan Janairun 1954 a jihar inda aka zabe shi a matsayin sanata a shekarar 1999, cewar Wikipedia.

Sodangi wanda lauya ne a Najeriya ya shiga makarantar lauyoyi ta Najeriya a jihar Legas a watan Mayun shekarar 1984.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Marigayin wanda ya shafe shekaru 12 a kujerar ya ci gaba da rike mukamin tun 1999 har shekarar 2011, Vanguard ta tattaro.

Sarkin Dikko-Enagi ya rasu a Neja

A baya, mun ruwaito maku cewa sarkin yankin Dikko-Enagi, Alhaji Muhammad Egba Enagi ya bar duniya.

Marigayin kuma shi ne mahaifin matar Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja, Hajiya Fatima Bago.

Marigayin ya rasu a ranar Asabar 9 ga watan Maris ya na da shekaru 90 inda aka binne shi jiya Lahadi 11 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel