Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata, Ya Fadi Matakin da Zai Dauka

Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata, Ya Fadi Matakin da Zai Dauka

  • Yayin da aka dakatar da Sanata Abdul Ningi, gwamnatin jihar Bauchi ta yi martani kan lamarin da ya faru
  • Gwamna Bala Mohammed na jihar ya ce ya na tare da Ningi a kowane lokaci musamman idan abin da ya ke kai gaskiya ne
  • Gwamnan ya bayyana haka a yau Laraba 13 ga watan Maris yayin taron majalisar zartarwar jihar a birnin Bauchi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta nuna goyon bayanta ga dakataccen Sanatan jihar, Abdul Ningi.

Gwamna Bala Mohammed shi ya bayyana haka yayin taron majalisar zartarwa a yau Laraba 13 ga watan Maris, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Shehu Sani ya lissafo matsalolin da sanatan zai fuskanta, ya fadi mai cetonshi

Gwmanan PDP ya ce ta na tare da Sanata Ningi bayan dakatar da shi
Gwamna Bala ya nuna goyon baya ga Sanata Ningi kan dakatar da shi a Majalisa. Hoto: Bala Mohammed, Abdul Ningi.
Asali: Facebook

Matsayar Gwamna Bala kan Sanata Ningi

"Jiya na ji bakin ciki bayan dakatar da daya daga Sanatoci masu kyau a Bauchi saboda ya tsaya a kan gaskiya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban san menene za mu yi ba amma za mu yi magana ta sirri domin neman mafita kan lamarin."
"Ina tare da shi a ko da yaushe wannan ita ce matsayarmu musamman idan abin da ya ke fada gaskiya ne."

- Bala Mohammed

Muhawara a Majalisa kan Abdul Ningi

Wannan martanin na zuwa ne bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yi na cushe a kasafin kudin shekarar 2024, cewar Barrister NG.

Bayan cece-kuce a Majalisar kan zargin da sanatan ya yi, daga bisani Sanatoci da dama a Majalisar sun goyi bayan dakatar da shi har na tsawon watanni.

Majalisar ta shiga rudani bayan wani Sanata ya yi zargin nuna wariya a rabon kudi musamman daga bangaren manyan Sanatoci a Majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

An hargitse a Majalisa kan zargin Sanata Ningi, an fifita manyan Sanatoci wurin rabon kudi

An dakatar da Sanata Abdul Ningi

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi bisa zargin da ya yi na yin cushe a kasafin kuɗi na 2024.

An dakatar da Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar mahawarar da aka yi a zauren Majalisar.

Wannan na zuwa ne bayan Ningi ya yi zargin cewa cushen da aka yi a kasafin kudin zai illata kasar Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel