Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Kamu da Son Kujerar Shugabancin Jam'iyyar Ta Kasa, Ya Fadi Dalillai

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Kamu da Son Kujerar Shugabancin Jam'iyyar Ta Kasa, Ya Fadi Dalillai

  • Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin PDP
  • Suswam wanda tsohon sanata ne da ya wakili Benue ta Arewa maso Gabas ya bayyana haka ne a jiya Asabar 16 ga watan Maris
  • Ya ce bisa doka har yanzu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya bayan hukunci kotu kan sahihancin Dakta Iyorchia Ayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya nuna sha'awar neman kujerar shugaban jam'iyyar PDP.

Tsohon gwamnan wanda tsohon sanata ne da ya wakili Benue ta Arewa maso Gabas ya nuna sha'awar maye gurbin Dakta Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Kakakin kwamitin kamfen Atiku ya faɗi muhimman abubuwa 2 da Najeriya ke buƙata kafin zaɓen 2027

Tsohon gwamnan PDP ya nuna sha'awar shugabancin jam'iyyar ta kasa
Tsohon Gwamna, Gabriel Suswam ya nuna sha'awar kujerar shugaban jam'iyyar PDP. Hoto: Gabriel Suswam.
Asali: Twitter

Yaushe Suswam ya nuna sha'awar kujerar PDP?

Suswam ya bayyana haka ne a birnin Makurdi na jihar Benue yayin ganawa kwamitin ayyuka na jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda hadiminsa a bangaren yada labarai, Bede Bartholomew ya fitar, sanatan zai karasa wa'adin Ayu ne da kotu ta yi hukunci a kai.

Bede ya tabbatar da cewa Suswam ya samu tarba mai kyau daga kwamitin jami'yyar a jihar.

Ya kara da cewa Suswam ya gana da masu ruwa da tsaki na jamiyyar a karamar hukumar Katsina-Ala inda ya fada musu muradinsa.

Wadanda suka halarci taron jam'iyyar

"A yau (Asabar) masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP a Katsina-Ala sun yi ganawa a gidan Gabriel Suswam."
"Ganawar karkashin jagorancin mataimakin shugaban yanki na jam'iyyar, Azua Ashongo ya samu halartar manyan baki."
"Cikin wadanda suka halarta har da Sanata Suswam inda ya bayyana musu sha'awar neman shugabancin jam'iyyar wanda a bisa doka har yanzu ta na Arewa ta Tsakiya."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

- Gabriel Suswam

Sanarwar ta ce daga cikin wadanda suka halarci taron akwai dan takarar gwamna a zaben 2023, Titus Uba.

Sudan sun hada da mamban kwamitin amintattu, Margaret Icheen da sakataren yanki, Maurice Tsav da tsohon minista, Farfesa Nicholas Ada.

An kira Gwamna Caleb ya koma APC

Kun ji cewa an bukaci Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato da ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

APC da ke Arewa ta Tsakiya ita ta bukaci hakan inda ta ce hakan zai kara masa daraja a idon al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel