Arewa
Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa, harin da ta kai ta sama ya halaka shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Kachallah Damina, da mayakansa da dama.
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kubutar da mutane 16 daga hannun 'yan ta'adda a kauyen Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Tsohon dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Hamma Saleh ya ba shugabannin jam'iyyar a jihar kyautar kudi har N7.8m domin yin azumi cikin walwala.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya ƙaddamar da fara rabon kayayyakin agaji ga talakawa, gajiyayyau, marayu, mata da matasa karo na biyu a faɗin jihar ranar Litinin.
Gwamna Mai Mala Buni ya amince da kashe Naira miliyan 100 na ciyar da marasa galihu abinci a kowane rana har karshen watan azumin Ramadan a jihar Yobe.
Gidauniyar fitaccen dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote ta sanar da cewa a kullum ta na ciyar da mutane fiye da 10,000 a Kano da kewaye yayin ake azumi.
Mahara sun yi ajalin Dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki kafin daga bisani suka hallaka shi.
Mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwa da ke jihar Sokoto inda ta kone kadarorin miliyoyi wanda har zuwa yanzu ba a tantance asarar da aka yi ba.
Yayin da Shugaba ta ba umarnin bude iyakokin Najeriya da Nijar, hukumar Kwastam a yankin jihar Kebbi ta bude iyaka da ke Kamba domin inganta kasuwanci.
Arewa
Samu kari