Ramadan: Yadda Gidauniyar Dangote Ke Ciyar da Musulmai 10,000 a Kullum a Kano

Ramadan: Yadda Gidauniyar Dangote Ke Ciyar da Musulmai 10,000 a Kullum a Kano

  • Yayin da ake fama da halin kunci a watan Ramadan, Gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ta na ciyar da mutane 10,000 a kullum
  • Gidauniyar ta na ciyar da mutanen ne a kullum a birnin Kano da kewaye domin rage radadin halin kunci da jama’a ke ciki
  • Jami’ar Gidauniyar, Samira Sanusi ita bayyana haka a cikin watan sanarwa a yau Litinin 18 ga watan Maris a birnin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ta na ciyar da marasa karfi akalla 10,000 kullum a jihar Kano.

Gidauniyar ta kuma raba buhunan shinkafa miliyan daya wanda kudinsu ya kai N13bn a dukkan jihohi 36 da birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dinke ɓarakar da ta kunno kai a APC, an sauya mataimakin dan takarar gwamna

Yayin da ake fama a watan Ramadan, Gidauniyar Dangote ta kawo wa jama'a dauki
Gidauniyar Dangote ta na ciyar da mutane 10,000 a da Ramadan a Kano. Hoto: Dangote Foundation.
Asali: Facebook

Dalilin ciyarwa da Gidauniyar Dangote ke yi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar Gidauniyar, Samira Sanusi ta fitar a yau Litinin 18 ga watan Maris a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samira ta ce Gidauniyar ta dauki wannan matakin ne domin rage radadin wahala da ake ciki a fadin Najeriya baki daya, cewar Tribune.

Ta ce ana raba biredi 20,000 a Kano da kuma 15,000 a Legas duk rana wanda aka fara ciyar da al’umma tun a 2020 lokacin annobar Korona.

Jami'ar ta kara da cewa daga cikin abincin da ake dafa wa domin watan Ramadan akwai shinkafa dafa-duka da shinakafa da miya da taliya.

Sauran ayyukan alherin Gidauniyar Dangote

Sauran sun hada da doya da wake da naman kaza da na saniya da kuma kayan ruwa wanda ake ba kowane mutum daya, cewar The Source.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin kudi: Sanata ya tabbatar da karbar Naira biliyan 1 na ayyukan mazaba

Har ila yau, ta ce su na raba abincin ne a masallatan Juma’a da gidan yari da kan tituna da gidan marayu a birnin Kano da keyawe.

Samira ta ce Gidauniyar ta na ciyar da marasa karfi da masu bukata ta musamman a boye wanda ya fi shekaru 30 da farawa.

Gwamna Aliyu ya gwangwaje ma’aikata

Kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ba ma’aikatan jihar rabin albashinsu kyauta saboda watan Ramadan.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne domin tallafawa ma’aikatan Sokoto wajen gudanar da azumin Ramadan cikin walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel