Gwamnan Arewa Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Mutuwar Ɗaliban Jami'a a Wurin Wawar Shinkafa

Gwamnan Arewa Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Mutuwar Ɗaliban Jami'a a Wurin Wawar Shinkafa

  • Gwamna Abdullahi Sule ya umarci hukumar jami'ar jihar Nasarawa da jami'an tsaro su yi bincike kan mutuwar ɗalibai 2 a wurin rabon tallafi
  • Ɗalibai mata biyu ne aka tabbatar sun mutu a wurin wawason tallafin shinkafa da gwamnatin Nasarawa ta shirya rabawa ɗaliban jami'ar
  • Mataimakin gwamnan jihar, Emmanuel Agbadu Akabe, ya ziyarci jami'ar domin gane wa idonsa ainihin abin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai mata biyu na jami’ar jihar da ke Keffi.

Bayan ɗalibai biyu da suka rasa rayuwarsu, a halin yanzu akwai wasu ɗalibai akalla 23 da ke kwance a asibiti suna karɓan magani, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dalibai sun mutu a wani turmutsitsi a wurin rabon tallafin shinkafa a jami'ar Arewa

Kofar shiga jami'ar Nasarawa.
Za a bincike musabbabin abin da ya jawo mutuwar ɗalibai a Nasarawa Hoto: Nasarawa State University, Keffi
Asali: Facebook

Ainihin abin da ya faru

Tun farko, hukumar jami'ar jihar Nasarawa ta karɓi kayan tallafi daga gwamnatin jihar domin rabawa ɗalibai da nufin rage musu wahalhalin matsin tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai yayin rabon tallafin, wasu ɗalibai suka ci ƙarfin jami'an tsaro da ke wurin, suka dakawa shinkafa da sauran kayayyakin wawa, hakan ya haddasa turmutsutsi.

Garin haka ne biyu daga cikin ɗaliban jami'ar suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka, sauran kuma suka kwashe kayan abincin gaba ɗaya.

Sule ya ɗauki mataki

A wata sanarwa da ya fitar dangane da lamarin, Gwamna Sule ya kaɗu da mutuwar ɗaliban jami'ar sanadiyyar wawason kayan abinci.

Sanarwan ta ce:

"Ina addu'ar Allah ya sa ransu ya samu salama, muna mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan mamatan a daidai wannan lokaci na alhini. Abun ba dadi datse rayuwar matasa a irin wannan ibtila'in.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

"Tuni mai girma gwamna ya umarci hukumar makarantar da hukumomin tsaro su fara bincike kan abin da ya jawo wannan lamari domin zaƙulo masu hannu."

Mataimakin gwamna ya ziyarci wurin

Gwamnan ya kuma yi kira da a kwantar da hankula yayin da ya jaddada cewa gwamnatin jihar Nasarawa karkashin jagorancinsa ba za ta shagala ba, za a ci gaba da rabon tallafi.

Mataimakin gwamnan jihar, Dakta Emmanuel Agbadu Akabe, ya ziyarci jami’ar domin gane wa idonsa gaskiyar abin da ya faru, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Gwamnoni 16 sun goyi bayan kafa ƴan sandan jihohi

A wani rahoton kuma Aƙalla gwamnoni 16 ne suka ayyana goyon bayan kafa rundunar ƴan sandan jihohi yayin da matsalar tsaro ke kara karuwa a Najeriya.

Majalisar tattalin arzikin ƙasa ta tabbatar da haka ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 21 ga watan Maris bayan kammala taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel