Kaduna: Rundunar Soji Ta Samu Gagarumar Nasara Bayan Ceto Mutane 16 Hannun Miyagu

Kaduna: Rundunar Soji Ta Samu Gagarumar Nasara Bayan Ceto Mutane 16 Hannun Miyagu

  • Yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar kan hare-haren 'yan bindiga, sojoji sun ceto mutane 16 a jihar Kaduna
  • Rundunar ta kai samame maboyar maharan inda ta fatattake su tare da ceto mutane 16 da maharan suka sace
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru a jihar bayan arangama da maharan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta ceto wasu mutane 16 da aka sace a jihar Kaduna.

Rundunar ta yi nasarar ceto su ne a hannun 'yan bindiga a kauyen Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru a jihar.

Dakarun soji sun kubutar da mutane 16 daga hannun 'yan bindiga
Sojoji sun ceto mutane 16 daga hannun miyagu a jihar Kaduna. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Nasarar da sojoji suka samu a Kaduna

Kara karanta wannan

DHQ ta fitar da cikakken jerin sunaye da hotunan dakarun sojojin da aka kashe a jihar PDP

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X kan wannan babbar nasara da ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yayin da rundunarmu ta isa maboyar maharan, jami'anmu sun fatattaki 'yan bindigar tare da ceto mutane 16 a daga hannunsu."
"Jami'anmu su na ci gaba da kutsawa cikin daji domin fatattakar 'yan bindigar tare da ceto wasu da aka sace."
"Hafsan sojin Najeriya, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja ya yabawa rundunar kan wannan namijin kokari da tayi na ceto wadanda aka sace."

- Rundunar soji

Lagbaja ya hore su da su ci gaba da kokarin ceto sauran garuruwa da ke fama da hare-haren da bindiga.

'Yan bindiga sun sace dalibai 287 a Kaduna

Wannan na zuwa ne bayan mahara sun durfafi makarantar Kuriga a jihar Kaduna tare da sace dalibai 287 yayin harin.

Kara karanta wannan

Mataki mai karfi da hukumar soji ta dauka a Delta bayan kashe mata jami'ai 16

Jama'a da dama a kasar sun yi Allah wadai da harin inda suka bukaci hobbasa daga gwamnati domin ceto daliban cikin ruwan sanyi.

'Yan bindiga: Gumi ya yi maganar sulhu

Kun ji cewa, Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa jami'an tsaro sun san inda maboyar 'yan bindiga ta ke a Arewacin Najeriya.

Gumi ya tabbatar da haka ne inda ya ce tare suke zuwa wurin 'yan ta'addan lokacin da ake ƙoƙarin sulhu da su.

Har ila yau, malamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi afuwa ga 'yan bindigar kamar yadda ta yi a yankin Neja Delta a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel