Sokoto: An Barke da Murna Yayin da Almajirai 15 da Aka Sace Suka Kubuce Daga Miyagu

Sokoto: An Barke da Murna Yayin da Almajirai 15 da Aka Sace Suka Kubuce Daga Miyagu

  • Makonni biyu bayan sace daliban tsangaya 15 a jihar Sokoto, a yanzu sun samu kubuta daga hannun 'yan bindiga
  • Dalibai guda 15 din an sace su ne a kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada a jihar da ke Arewa maso Yamma
  • Wannan na zuwa ne yayin da yankin ke fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Daliban makarantar tsangaya da aka sace guda 15 sun samu nasarar dawowa gida a jihar Sokoto.

An sace daliban ne a kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada a jihar a makwanni biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe sabon ango a harin kasuwar Arewa, an samu karin bayani

Daliban tsangaya da aka sace kun shaki iskar 'yanci
Daliban tsangaya 15 da aka sace a Sokoto sun kubuta daga hannun 'yan bindiga. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Facebook

Yadda aka sace daliban tsangaya a Sokoto

An yi garkuwa da Almajiran ne yayin da su ke gudun tsira domin tsira daga harin 'yan bindiga, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai makarantar, Liman Abubakar ya tabbatar da cewa an sace daliban ne da misalin karfe daya na dare.

Ya ce maharan sun farmaki kauyen inda suka hallaka wani mutum daya kuma suka sace wata mata, cewar TheCable.

Mai tsangayar ya yi bayani faruwar lamarin

Liman ya ce lokacin da maharan ke kai harin ne suka hango dalibansu su na kokarin guduwa sai suka yi garkuwa da su.

"Yayin da suke kokarin tafiya ne su ka hango dalibanmu suna neman tserewar sai suka yi garkuwa da mafi yawa daga ciki."
"Muna lissafin sun dauke 15 kuma muna ci gaba da lissafi."

- Liman Abubakar

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

Har ila yau, mamban da ke wakiltar Gada ta Gabas, Kabiru Garba ya ce shi ma ya samu labarin garkuwa da daliban da misalin karfe biyu na dare.

Mahara sun sace dalibai a tsangaya

Kun ji cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar Alkur'ani a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Maharan sun farmaki kauyen Gidan Bakuso ne da ke karamar hukumar Gada a jihar makwanni biyu da suna wuce.

Wannan na zuwa ne bayan sace wasu dalibai 285 a jihar Kaduna inda 'yan bindigan suka bukaci kudin fansa har N1bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel