Ramadan: Dan Takara a PDP Ya Gwangwaje Shugabannin Jam’iyyar da N7.8m

Ramadan: Dan Takara a PDP Ya Gwangwaje Shugabannin Jam’iyyar da N7.8m

  • Yayin da ake fama da kunci a wannan wata na Ramadan, jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Hamma Saleh ya yi abin alheri
  • Hamma Saleh wanda ya yi takarar gwamna a jam'iyyar ya gwangwaje shugabannin jam'iyyar da kudi N7.8m domin azumi cikin walwala
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu daga cikin shugabannin PDP a wasu kananan hukumomi kan rabon kuɗin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Tsohon dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Hamma Saleh ya ba shugabanin jam'iyyar a jihar goron azumi.

Hamma Saleh ya ba manyan jam'iyyar PDP a jihar N7.8m domin su yi azumin watan Ramadan cikin walwala.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sake cin karo da babbar matsala kan takarar da yake nema karo na 2

Jigon PDP ya yi abin alheri bayan gwangwaje 'yan jam'iyyarsa da makudan kudi
Hamma Saleh ya ba shugabannin PDP kudi a Gombe Hoto: @_hauwah.
Asali: Instagram

Sakataren jam'iyyar PDP a jihar ya yi godiya

Jigon PDP ya kuma ba dattawa da shugabannin jam'iyya a kananan hukumomi kyautar makudan kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren jam'iyyar PDP a jihar, Adamu Abubakar shi ya bayyana haka inda ya yi godiya ga jigon jam'iyyar a jihar, cewar Tribune.

Adamu ya godewa Hamma Saleh kan wannan gudunmawa da ya bayar inda ya yi masa adudu'ar sakayya daga ubangiji.

Sakataren y ce tabbas wannan taimako zai taimakawa shugabannin jam'iyyar musamman a wannan lokaci na azumi.

Ya kara da cewa kyautar ta zo a dai-dai lokacin da ake bukatarta ganin irin halin kunci da 'yan kasar ke ciki, cewar Leadership.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu daga cikin shugabannin PDP a wasu kananan hukumomi kan rabon kuɗin

Shugaban jam'iyyar PDP a karamar hukumar Akko a jihar, Baba S. Fulani ya tabbatar da samun kasonsu ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Zai yi wahala APC ta kai labari, jiga-jigan jam'iyya sun gargadi Tinubu kan halayen Minitansa

"Tabbas sakon ya iso mu ba tare da matsala ba , mun yi farin ciki da wannan kyauta matuƙa."

- Baba S. Fulani

Har ila yau, shugaban jam'iyyar a Dukku, Abdulkadir Yusuf wanda aka dakatar saboda wasu matsaloli ya tabbatar da samun sakon.

Ya ce tabbas ya samu labarin sakon ya zo gare su ta hannun mukaddashin shugaban jam'iyyar a yanzu.

Gwamna Inuwa ya gwangwaje Hajara Danazumi

Har ila yau, ana da labari a jihar Gombe, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar ya gwangwaje daliba Hajara Ibrahim Dan'azumi da kyautar kudi.

Gwamnan ya ba dalibar kyautar kudi har naira miliyan biyar saboda kokarinta a gasar musabaka ta duniya.

Wannan na zuwa ne bayan dalibar ta yi nasara a gasar duniya da aka yi a kasar Jordan.

Suswam na neman shugabancin PDP

A baya, mun ruwaito muku cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya nuna sha'awar neman kujerar shugaban jam'iyyar PDP.

Tsohon gwamnan wanda tsohon sanata ne da ya wakili Benue ta Arewa maso Gabas ya nuna sha'awar maye gurbin Dakta Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel