Gaskiya Ta Bayyana: Jigon LP Ya Bayyana Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Yi Buda-Baki da Musulmai

Gaskiya Ta Bayyana: Jigon LP Ya Bayyana Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Yi Buda-Baki da Musulmai

  • Ziyarar da Peter Obi ya kai wani masallaci kwanan nan ya jawo cece-kuce da hasashen siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027
  • Wani hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa Obi bai kai ziyarar haka banza ba
  • Sai dai, Yunusa Tanko mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya yi martani mai daukar hankali kan maganar

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Yunusa Tanko, kakakin majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Labour, ya fito ya goyi bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar a zaben 2023, a cece-kucen da ake na halartarsa buda bakin azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya yi ƙus-ƙus da Ministan Tinubu da jigon APC a Kano, bayanai sun fito

Obi ya ziyarci babban masallacin da ke Maraba-Nyanya a Abuja, domin halartar liyafar cin abincin buda baki da al'ummar Musulmi.

Dalilin da yasa Peter Obi ya yi buda baki da Musulmai
Tanko Yunusa ya fadi dalilin da yasa Obi ya yi buda-badi da Musulmai | Hoto: @Elvispatrick20
Asali: Twitter

Bashir Ahmad ya tabo batu kan ziyarar Obi Abuja

Bashir Ahmad, wanda tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kan harkokin yada labarai, ya nuna shakku kan manufar Obi ta rabar 'yan Arewa, inda ya nuna cewa yana da wani shiri na siyasa a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmad ya dasa ayar tambaya kan dalilin da zai sa Obi ya ki halartar taron buda baki a jiharsa ta Anambra tare da zuwa Arewa.

Martanin Tanko ga kalaman Bashir Ahmad

Da yake mayar da martani ga zarge-zargen Bashir, Tanko ya bayyana cewa, hasashen Obi ya kai ziyarar ne da manufa ta siyasa ba daidai ba ne.

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

“Idan ka duba tarhinsa, za ka gani a bayyane ceewa dabi’a ce a gare shi ya rika cudanya da jama’a, musamman ma talakawa. Rayuwarsa kenan. Ba yanzu ya fara haka ba.
“Sau da yawa, ya sha ziyartar ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya kuma ya yi cudanya dasu. A lokacin da yake gwamnan Anambra, ya yi buda-baki da jama’a a Onitsha."

Dag nan kuma ya bayyana halin tausayi da kaunar jama'a irin na Obi da kuma yadda yake son jama'a.

Ziyarar Obi ga masu azumi

A wani labarin, an sake ganin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi a yana buda-bakin azumi a tare da musulmi.

A ranar Talata, 19 ga watan Maris aka gano tsohon gwamnan jihar Anambra a babban masallacin Suleja da ke kan hanyar Suleja zuwa Kaduna a jihar Neja.

An ganshi yana zaune a sahun gaba cikin daruruwan musulmi, yana sauraren tafsirin Al-Kur'ani da limamin masallacin yake gabatarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel