Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso
'Yan sanda sun baza dakaru a lunguna da sako a Kano. Masoyan Abba Kabir Yusuf da 'Yan Gawuna Has Arrived ba su iya fita zanga-zangar da su ka yi niyyar yi a Kano ba.
Kotun koli kurum za ta iya raba gardama a shari'ar zaben Kano na 2023. Wole Olanipekun ya ce a doka babu gyaran da za a iya yi wa takardun hukuncin zaben Kano yanzu
Ana tsoron tashin hankali ya barke a garin Kano domin kabilu sun fara tsorata ganin zanga-zanga sun barke a dalilin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf a kotu.
Farfesa Chidi Odinakalu ya ce akwai alaka tsakanin Alkalin da kuma shugaban Alkalin Alkalai na kasa watau Kayode Ariwoola, mun gano akwai alakarsu da manya a APC.
Bayanan takardun shari’ar Abba v Gawuna ba kuskure ba ne a ra'ayin wasu. Chidi Odinkalu ya fadawa duniya cewa kotun daukaka kara ba za ta iya yin kwaba ta gyara ba.
Kingsley Chiedu Moghalu ya nuna hukuncin zaben Gwamnan Kano ya na neman tada zaune tsaye a sakamakon tsige Abba Kabir Yusuf, an ji yana kukan hukumomi sun lalace.
Labari ya zo daga Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano cewa Jami’an tsaro sun damke wasu mutane da ake zargin sun fito yin zanga-zanga saboda hukuncin zaben gwamna.
A yanzu wasu magoya bayan NNPP suna murnar kotun daukaka kara ta ba su gaskiya wajen rubuta hukuncin shari’ar Kano, amma lauyoyi sun ce ba haka abin yake ba.
NNPP ta fusata, inda shi kuma Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara yayin da aka fara zanga-zanga a Kano saboda hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar a ranar Juma'a.
Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso
Samu kari