Abba Gida Gida: Mata Sun Barke da Zanga Zanga a Kan Tsige Gwamnan Kano a Kotu

Abba Gida Gida: Mata Sun Barke da Zanga Zanga a Kan Tsige Gwamnan Kano a Kotu

  • Mata da-dama sun fito kan titunan garin Kano domin sukar hukuncin shari’ar zaben Gwamna da aka yi a kotu
  • Masu kaunar Gwamna Abba Kabir Yusuf sun zargi Alkalai da rashin adalci wajen ba APC mulkin jihar Kano
  • Har a kudancin Najeriya, an samu ‘yan darikar Kwankwasiyya da masoyan Abba da su ka shirya zanga-zanga

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Akalla mata dubu ne su ka yi zanga-zanga a titunan garin Kano domin nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin shari’ar zabe.

A wani rahoto na The Guardian, an ji cewa matan sun yi tir da yadda alkalan kotun daukaka kara su ka tsige Abba Kabir Yusuf a kotu.

Abba.
Abba Gida Gida wajen kamfe Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Masoyan Abba sun hau tituna

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

Wadannan mata sun rika yawo kan tituna suna rera wakokin gwamna Abba Kabir Yusuf, suka nufi babban ofishin jami’an ‘yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matan sun gabatar da wasiku da sakonni na rashin na’am da hukuncin shari’ar zaben gwamnan Kano, inda aka tsige Abba Gida Gida.

Jaridar ta ce wannan ne karon farko da mata za su yi dandazo a kan titi, suna neman a tabbatar da nasarar NNPP a zaben gwamna na 2023.

Menene ya jawo zanga-zanga a Kano?

Wata mai suna Hajiya Rabi Hotoro ta ce abin da ya jawo zanga-zangar shi ne kira ga masu ruwa da tsaki su yi wa mutanen Kano adalci.

Magoya bayan Abba sun zargi alkalai da yin son kai saboda an rusa nasarar NNPP, aka ce Nasiru Gawuna na APC ne halataccen gwamna.

Da ‘yan jarida su ka yi hira da wata Amina Adam Sulaiman da ke zama a Kano, ta shaida sai dai a kashe su a wajen kare Abba Gida Gida.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun tura gargadi ga jam'iyyun APC, NNPP kan shirin zanga-zanga a jihar

"Sai dai a raba mu da numfashinmu a kan kuri'ar da mu ka ba Abba gida-gida, ba gudu babu ja da baya!"

- Wata mai goyon Abba

Zanga-zangar Abba a Ibadan

Punch ta ce a garin Ibadan da ke jihar Oyo, masu kaunar gwamnan Kano sun shirya zanga-zanga a filin wasa na Lekan Salami a jiya.

Masoya da ‘Yan Kwankwasiyya sun fito su na ihun ‘Kano Abba Muka Zaba’ inda su ka yi Allah-wadai da kotun zabe da na daukaka kara.

'Yan sanda sun baza jami'ai a Kano

Amma kafin nan an ji labari cewa masoyan Abba Kabir Yusuf da 'Yan Gawuna Has Arrived ba su iya fita zanga-zanga a ranar Asabar ba.

‘Yan siyasa da magoya bayan sun yi niyyar yin addu’o’i, zanga-zangar lumana da taron murna, amma hakan bai yiwu ba saboda tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel