Jami’an Tsaro Sun Cika Ko Ina, NNPP da APC Sun Hakura da Zanga Zanga a Kano

Jami’an Tsaro Sun Cika Ko Ina, NNPP da APC Sun Hakura da Zanga Zanga a Kano

  • Da alama Jami’an tsaro sun yi nasarar hana zanga-zangar da ‘yan NNPP da APC su ka shirya za su yi a yau
  • Zuwa yanzu babu wanda ya fita kan titi domin nuna bakin ciki ko murnar hukuncin zaben Gwamnan Kano
  • Wasu jagororin jam’iyyun APC da NNPP sun ce sun hakura da fita kan tituna ne saboda tsare rayuka da dukiya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Jami’an tsaro sun cika birnin Kano a yau Asabar da ‘yan siyasa da magoya baya su ke shirin fita-zangar lumana.

A rahoton da Daily Trust ta fitar, an fahimci cewa ba a iya ganin masu zanga-zanga kamar yadda aka tsara za ayi a yau ba.

NNPP.
Masoyan Abba Gida Gida da NNPP a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Magoya bayan jam’iyyun NNPP da na APC da su ka tsaida yau a matsayin ranar hawa kan tituna, duk ba su iya yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Mata sun barke da zanga-zanga a kan tsige Gwamnan Kano a Kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon hukuncin zaben gwamnan jihar Kano ya jawo rashin jituwa musamman wajen magoya bayan darikar Kwankwasiyya.

Abin da 'Yan APC da NNPP su ke fada a Kano

Mansur Haruna Dandago wanda hadimi ne ga Nasiru Yusuf Gawuna ya shaidawa jaridar cewa sun hakura da zanga-zangarsu.

Abin da Alhaji Mansur Dandago ya ce sun yi la’akari da shi kuwa shi ne rayuwa da dukiyar al’umma, saboda haka sai su ka fasa.

Abubakar Moriki wanda ya na cikin jagororin NNPP a karamar hukumar Tarauni ya ce jagororinsu sun umarce su dakatar da shirin.

Moriki yake cewa da a zubar da jinin wani a Kano, sun zabi a karbe gwamnati a hannunsu.

Wadanda ke tare da Abba Kabir Yusuf su na ganin kotu ba ta yi adalci wajen tsige gwamnan jihar Kano daga kujerar mulki ba.

A gefe guda, masoyan APC da Nasir Yusuf Gawuna su na farin ciki da hukuncin kotun, sun shirya yin taron murna a yau.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun tura gargadi ga jam'iyyun APC, NNPP kan shirin zanga-zanga a jihar

Malam Shu'aibu Babu wani mazaunin garin Kano ne, wanda ya shaidawa Legit cewa har zuwa yanzu ba a fita zanga-zanga ba.

Wadanda mu ka tattauna da su sun nuna jama'a ba su ji dadin hukuncin kotun ba.

Masoyan NNPP, Kwankwasiyya da jama'a za su yi zanga-zanga?

Aliyu Isa Aliyu wanda shi ne Sakataren harkar kudi na jam’iyyar NNPP a Kano ya ce nan gaba za su yi zanga-zangar da aka shirya.

“Idan lokacin yin zanga zangar lumanar yayi, In sha Allahu za mu fito da mu, da yan uwan mu da ma duk wanda muka isa da shi dan kare abun da muka zaba a jihar Kano. Alhaji Abba K Yusuf shi al'umma suka zaba, shi suke so, a bar musu zabin su.
Ba duka, ba zagi kuma ba satar abin kowa. Dokar qasa ta bamu damar mu aiwatar da ita cikin lumana. Babu wata doka da tace a hana mutane nuna rashin jin dadin su ta hanyar aiwatar da zanga zangar lumana.

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Tashin hankali yayin da APC da NNPP suka shirya gagarumin abu rana ɗaya a Kano

Wannan gwagwarmayar ba ta dan NNPP ko kwankwasiyya bace. Ta shafi duk wani dan Kano mai kishin cigaban jihar

- Aliyu Isa Aliyu

'Yan sanda sun kama mutane a Kano

Jami’an ‘yan sanda sun kara tabbatar da cewa ba za su yarda da zanga-zanga a Kano ba, saboda haka ne aka cafke mutane bakwai.

Amnesty International ta goyi bayan wadanda su ka fito zanga-zanga saboda rashin gamsuwa da hukuncin kotu, ta bukaci a sake su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel