Abun Al Ajabi
Wani dan Najeriya ya maganatu kan yadda ya tsinci kansa yana kwana a karkashin gadar Oshodi da ke jihar Lagas bayan ya shafe shekaru 21 a Amurka.
Muhammadu Buhari a hirarsa ta farko tun bayan saukarsa daga karagar mulki kimanin watanni shida da suka gabata, ya ce baya kewar barin kujerar shugabanci.
Wani shirin neman aure na bazata ya koma ya zama mummunan al’amari bayan budurwar ta kunyata saurayinta a bainar jama’a. Ta sharara masa mari mai zafin gaske.
Mai shari’a Hakeem Oshodi na wata babbar kotu a Legas, ya gargadi jama’a da su daina barin layoyi a kotunsa domin ba sa aiki kuma. Ya yi gargadin yayin zaman kotu.
Wata mata yar shekaru 30 da ta auri mahaifin kawarta mai shekaru 87 ta magantu kan yadda suka fada tarkon son junansu a ranar farko da suka hadu. Suna da yara biyu.
Wata mata wacce ke dauke da dabbare-dabbaren baki a fuskarta ta yadu bayan ta ba da labarin abun da ya haddasa mata haka. Jama’a sun tausaya mata a sashin sharhi.
Wani ƙaramin yaro Almajiri a jihar Bauchi ya yi garkuwa da wata ƙaramar yarinya a jihar Bauchi. Yaron dai ya shiga har gidan mahaifin yarinyar sannan ya sace ta.
Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kama wani matashi daga kauyen Madakiya da ke karamar hukumar Zangon Kataf kan kashe mahaifinsa saboda ya bayyana a mafarkinsa.
Da alama wani dalibi da ya yi asarar kudin karatunsa gaba daya a caca zai samu rangwame. Hakan ya kasance ne yayin da wani da ya ci N102m a caca ya waiwaye shi.
Abun Al Ajabi
Samu kari