Hotunan babban malamin Musulunci na zullewa hada jiki da yar TikTok ya ja hankali

Hotunan babban malamin Musulunci na zullewa hada jiki da yar TikTok ya ja hankali

  • Shahararren malamin Musulunci, Mufti Menk, ya yi fice a dandalin soshiyal midiya kan haduwarsu da yar barkwanci Taaooma
  • Wasu hotuna da Taaooma ta wallafa a soshiyal midiya na haduwarsu da Mufti Menk a ziyarar baya-bayan nan da ya kawo Najeriya ya haddasa cece-kuce
  • A wallafarta, Taaooma ta bayyana yadda malamin ya yi a lokacin da ta nemi daukar hoton 'selfie' tare da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yar wasan barkwanci a Najeriya, Maryam Apaokagi wacce aka fi sani da Taaooma, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa hotunanta tare da fitaccen malamin Musulunci Mufti Menk.

A kasan wallafar tata, Taaoma ta bayyana tattaunawar da ta yi da Mufti.

Taaooma ta dauki hoto tare da Mufti Menk
Hotunan babban malamin Musulunci na zullewa hada jiki da yar TikTok ya ja hankali Hoto: @_taaooma
Asali: Instagram

Yar wasan barkwancin da ta yi baiko kwanaki ta kuma bayyana yadda malamin addinin ya dunga zillewa hada jiki da ita cikin dabara yayin da ta nemi daukar hoton 'selfie' tare da shi.

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mufti Menk ya sanya jaka tsakaninsa da Taaooma

A cikin wallafar tata, Taaooma ta bayyana yadda malamin Musuluncin ya sanya wata yar jaka a tsakaninsa da ita.

Ta bayyana cewa malamin addinin ya ce ya yi hakan ne a matsayin alamar mutuntawa ga matarsa.

Sai dai kuma, a lokacin da wani matashi ya shiga cikinsu don daukar hoton 'selfie', Mufti Menk ya bar shi ya tsaya kusa da shi sabanin ita.

Taaooma ta rubuta:

"Mufti - Saboda matata, bari na sanya wannan jakar a nan."

Ga wallafar Taaooma a kasa:

Jama'a sun yi martani kan hotunan Taaooma da Mufti Menk

Dubi yadda jama'a suka yi martani ga wallafar Taaooma:

@Ademo_la:

"Mufti mafi soyuwa a gareni. A kullun yana tallata addinin Islama da duk damar da ta samu."

@uncletenshun:

"Ina matukar kaunar mutumin nan."

Kara karanta wannan

Miji ya zargi surukinsa hakimi, basarake a Kano da kashe masa aure tare da yunkurin tozarta shi

@tosinraj:

"Babu wanda zai hadu da Mufti Menk ba tare da ya yi farin ciki ba."

@amazingtundeh:

"Mufti baya so ya yi bayani har ya gaji."

@RealSheyi:

"Hatta da Sheik yana tsoron mata, Yallabai baya so ya yi bayani. Saboda akwai hujja❤."

Mufti ya taya dan kwallo murna

A wani labarin, mun ji cewa Mufti Menk ya taya kasar Argentina da kuma kyaftin din ta, Lionel Messi murnar lashe gasar cin kofin Duniya wanda aka kammala.

Mufti Menk wanda ya yi suna wajen yin wa’azi a kasashen Duniya, ya yi amfani da shafin Twitter, ya aika sakon murna ga wadanda suka yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng