Bidiyon Yadda Budurwa Ta Shararawa Saurayi Mari Bayan Ya Nemi Ta Aure Shi Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Yadda Budurwa Ta Shararawa Saurayi Mari Bayan Ya Nemi Ta Aure Shi Ya Girgiza Intanet

  • Shirin neman aure na bazata da wani matashi ya yi wa budurwarsa ya samu tangarda yayin da ta kunyata shi a bainar jama'a
  • Ya durkusa a bainar jama'a rike da zobe a hannunsa sannan ya nemi ta aure shi amma sai budurwar ta kwashe shi da mari
  • Abun da ya faru ya haddasa hargitsi a wajen faruwar lanmarin sannan mutanen soshiyal midiya sun dauki dumi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyon neman aure da aka samu tangarda ya bayyana a soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce a tsakanin al'umma.

Wani mai suna @cliifforrd, ya yada bidiyon yayin da yake al'ajabin abun da mutane za su aikata da sune abun da ya faru da matashin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

“Na zata ba zai yiwu ba”: Tsoho dan shekaru 87 ya fada tarkon son kawar diyarsa, ya yi wuff da ita

Budurwa ta shararawa saurayi mari a wajen neman aurenta
Bidiyon Yadda Budurwa Ta Shararawa Saurayi Mari Bayan Ya Nemi Ta Aure Shi Ya Girgiza Intanet Hoto: @cliifforrd
Asali: Twitter
"Da kaine wannan gayen, me za ka yi?" taken da ke jikin bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lura a cewa matashin ya durkusa rike da zobe domin neman aurenta a bidiyon, amma sai matar ta yi watsi da bukatarsa.

Bayan ta juya masa baya, ta matso kusa sannan ta sharara masa mari a fuska, lamarin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin mutanen da ke wajen da abun ya faru.

Wasu mutane da suka nuna damuwa sun gaggauta zuwa wajen da mutumin ke duke sannan suka bukaci ya tashi tsaye kan kafafunsa, yayin da budurwar ta bar wajen.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun caccaki budurwar kan abun da ta yi

@OluseunJose ya ce:

"Baaba, wannan yarinyar bata ma cancanci wannan jajircewar ba....
"Wadannan gayun da suka bukaci ya tashi tsaye sun sani, da ace abokina ne, zan sake sharara mai wani mari na farkawa."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fuskar wata mata ta sauya gaba daya bayan wani ya taba ta a wajen birne gawa

@Templegaurd ya ce:

"Kada ki amince da bukatata amma kada ki mare ni, tunda ba wai baki da hankali bane. Me yasa kake rokonta? Kamata ya yi ya zama neman iri, idan bata yi, ka kara gaba. Kana rokonta don gobe ta ce alfarma ta yi maka, ba alfarma kika yi mun ba. Nima wani kwaro ne."

@BlaccYsl:

"Jinjina ga mazajen da suka je suka daga shi lokacin da ake masa dariya."

Alkali ya gargadi masu barin layu a kotunsa

A wani labarin, mai shari'a Hakeem Oshodi na babbar kotu a Ikeja, Lagas, ya yi gagarumin gargadi ga jama'a.

Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, Oshodi ya yi gargadin cewa ya kamata mutane su daina ajiye masa layu a cikin kotunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel