“Da Na Koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari Ya Magantu Kan Zaryar da Wasu Ke Yi a Gidansa Na Daura

“Da Na Koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari Ya Magantu Kan Zaryar da Wasu Ke Yi a Gidansa Na Daura

  • A wata hira ta musamman, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gidansa na ta fuskantar 'tsangwama' daga mutanen da ke tururuwan zuwa gidansa na Daura
  • Buhari ya nuna cewa lamarin ya yi kamari ta yadda da ace ba'a kulle iyakar kasa mafi kusa ba, da ya bar Najeriya
  • Duk da haka, Buhari ya lissafa wani muhimmin abu daya - yancin tashi daga bacci a duk lokacin da ya ga dama, yana mai jaddada cewar bai yi kewar lokacin da yake mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Daura, jihar Katsina - Duk da komawa zama da ya yi a nesa da babban birnin tarayyar kasar, tsohon shugaban kasa Muhammdu Buhari ya bayyana cewa mutane na daukar motoci don kai masa ziyara a Daura.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su na da wuyar sha'ani' Buhari ya bayyana abu 1 da jawo matsala a gwamnatinsa

Buhari ya ce mutane na yi masa zarya a gidansa na Daura
“Da Na Koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari Ya Magantu Kan Zaryar da Ake Yi a Gidansa Na Daura Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya magantu kan masu kai ziyarar bazata Daura

Tsohon shugaban kasar a wata hira a NTA wanda aka watsa a daren Litinin, 20 ga watan Nuwamba, ya nuna cewa baya kewar kasancewarsa a kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya ce:

"Mutane na hayar motocin bas suna zuwa ganina lokaci zuwa lokaci. Na zata na yi nesa da Abuja amma duk da haka suna zuwa. Da na lula Nijar da ace boda a bude yake."

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, tsohon shugaban kasar ya yi karin haske kan yadda yake tafiyar da lokacinsa bayan shugabanci da kalubale na bazata da abubuwan da yake fuskanta.

Watanni shida bayan mika mulki ga magajinsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buhari ya magantu game da yadda baya kewar kasancewa shugaban kasa.

Ya bayyana cewa duk da ya yi iya bakin kokarinsa, hakan bai wadatar da yan Najeriya ba, inda ya bayyana ra’ayinsa kan wa’adin mulkinsa da kuma kalubalen da ya fuskanta, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Buhari ya ambaci babban rauni 1 da yake da shi wanda ya iya kawo cikas a mulkinsa

"Na yi imani ina iya bakin kokarina, amma duk da haka kokarina bai isa ba. Ina mamaki ko zan yi kewar abubuwa da yawa. Ina ganin ana tsangwamana,” in ji Buhari.

Buhari ya bayyana rauninsa

A wani labarin, mun ji cewa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nanata cewa ya yi bakin kokarinsa a shekaru takwas da ya yi a ofis.

Amma duk da kokarin da yake ganin ya yi a kan mulki, This Day ta rahoto shugaban ya na mai cewa bai san ko ya iya cin ma nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel