Tirƙashi: Yadda Yaro Ɗan Shekara 9 Ya Yi Garkuwa da Yarinya Ƴar Shekara 5 a Bauchi

Tirƙashi: Yadda Yaro Ɗan Shekara 9 Ya Yi Garkuwa da Yarinya Ƴar Shekara 5 a Bauchi

  • Wani ƙaramin yaro ɗan shekara tara ya yi garkuwa da wata ƙaramar yarinya ƴar shekara biyar a jihar Bauchi
  • Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar wacce ta bayyana yadda yaron ya sace yarinyar ta ce ya nemi a ba shi N5m a matsayin kuɗin fansa
  • Ta bayyana cewa yaron wanda almajiri ne yanzu haka yana gidan gyaran hali na ƙananan yara a Bauchi bayan kotu ta yanke masa hukunci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban ƙananan yara, Hajara Gidado, ta bayyana yadda wani yaro Almajiri ɗan shekara tara, wanda aka ɓoye sunansa, ya sace wata yarinya ƴar shekara biyar a gidan mahaifinta.

Ta bayyana hakan ne a wajen bude taron horar da malaman Tsangaya da na Islamiyya na kwanaki biyu a ɗakin taro na Sa’ad Abubakar da ke Hajj Camp a Bauchi, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Yaron ɗan shekara 9 ya sace ƴar shekara 5 a Bauchi
Almajirin ya nemi a ba shi N5m a matsayin kudin fansa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yaron, a cewarta tun asali an kawo shi ne domin neman ilimin addinin Islama daga jihar Kano zuwa Magama Gumau da ke ƙaramar hukumar Toro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce daga baya ya samu tsohuwar wayar Android ta hanyar barace-barace sannan ya fara koyon yadda a ke aikata miyagun laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, rahoton Tribune ya tabbatar.

Ta wacce hanya ya sace ƙaramar yarinyar?

A kalamanta:

"Wata rana yana cikin bara, ya isa wani gida, sai ya haɗu da wata yarinya ƴar shekara biyar, ya ɗauke ta ya kai ta wata makaranta a garin. Bayan wasu sa'o'i sai yarinyar ta ji yunwa, shi ma ya ji yunwa. Don haka sai ya zagaya domin neman abin da su biyun za su ci."
"Ya yi ƙoƙarin samun lambar wayar mahaifin yarinyar, wanda ya daɗe yana neman yarinyar. Almajirin ya kira mahaifinta ya ce ya kawo Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa. Mahaifin yarinyar yayi biris dashi."

Kara karanta wannan

Dan majalisa a Kano ya yi alkawarin biyan kudin maganin yarinya yar shekara 5 mai fama da cutar daji

"Da yamma ya yanke shawarar mayar da yarinyar gidan da ya ɗauke ta. A hanya sai ya gamu da mahaifinta, ya tambaye shi inda ya samo yarinyar, sai ya shaida wa mahaifin cewa ya yi garkuwa da ita, kuma tun da mahaifin bai kawo kudin da ya nema ba, sai ya yanke shawarar mayar da ita."

Ta ce mahaifansa da malamin da aka kawo shi domin yin karatun addini a wajensa, sun bar shi a gidan gyara hali na ƙananan yara na Bauchi, inda yake zaman gyaran hali bayan kotu ta yanke masa hukunci kan laifin da ya aikata shekara uku da suka gabata.

Ɗan Shekara 20 Ya Halaka Mahaifinsa

A wani labarin kuma, wani matashi mai shekara 20 a duniya, David Felix, ya salwantar da ran mahaifinsa saboda yana zuwa masa a mafarki a jihar Kaduna.

Felix ya yi zargin cewa mahaifinsa na zuwa masa a mafarki a matsayin tsuntsu mai dauke da fuskar mutum, yana kokarin cutar da shi, saboda haka bai da wani zabi da ya wushe ya kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng