Dan Caca da Ya Ciyo N102m Zai Taimakawa Dalibin da Yayi Asarar Kudin Karatunsa a Caca

Dan Caca da Ya Ciyo N102m Zai Taimakawa Dalibin da Yayi Asarar Kudin Karatunsa a Caca

  • Ga dukkan alamu matashin dalibin nan da ya rasa gaba daya kudin makarantarsa a caca ya kusa ya dara
  • Hakan ya kasance ne saboda wani dan Najeriya da ya ci naira miliyan 102 a caca ya amsa rokonsa a wajen al'umma
  • Dalibin ya roki yan Najeriya a soshiyal midiya a kan su taimaka masa, yana mai nuna nadamar amfani da kudin makarantarsa wajen buga caca

Wani dan Najeriya, wanda aka fi sani da Mr Bayo, yana shirin taimakon wani matashin dalibi wanda ya yi asarar kudin makarantarsa a caca.

Legit Hausa ta rahoto yadda wani dalibi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya ba da labarin yadda ya rasa kudin makarantarsa a harkar caca.

Dalibin da ya rasa kudin karatunsa a caca ya taki sa'a
Dan Caca da Ya Ciyo N102m Zai Taimakawa Dalibin da Yayi Asarar Kudin Karatunsa a Caca Hoto: @mrbayoa1, @yusufop21648411
Asali: Twitter

Rubutun nasa wanda ya goge a yanzu ya dauki hankalin Mr Bayo, wanda ya ci naira miliyan 102 a caca yan kwanaki da suka gabata.

Kara karanta wannan

‘Dan wasan fim zai mikawa Gwamna Abba rikon yaransa 2 saboda dakatar da shi

Da yake nuni ga rubutunsa, Mr Bayo ya bukace shi da ya tura masa da sako. Ya rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka tura mani da sakon DM."

Wasu mutane sun shawarci Mr Bayo da kada ya karfafawa matashin gwiwar ci gaba da dabi'arsa ta hanyar tura masa kudi sannan ya amsa da:

"Kwarai, yan kunne shine iya abun da nake son yi, rubuce-rubuce da zagin da aka yi masa kadai sun isa su yi masa illa. Ina ganin rubutu irin wannan kullun kuma ina yin biris amma wasu lokutan ilimantar da su na iya taka muhimmiyar rawa!"

Duba wallafar Mr Bayo a nan.

Jama'a sun yi martani ga bukatar Mr Bayo

@evilmadss ya ce:

"Na dade ina tambayarka 50k baka so ka amsa, na san abun da zan yi bari na je na buga caca da kudin makaranta na."

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

@honiseymoh ta ce:

"Abun haushin shine wanizai je ya sake aikata haka sannan ya zo yana roko.
"Ka taki sa'a a yau."

@SportybetArena ya ce:

"Wannan gayen ya taki sa'a sosai. Caca wani aljani ne dai. Idan baka da lissafi kana iya rasa komai."

Matashi ya buga caca da N400k

A wani labarin, mun ji cewa wani ɗalibi ɗan Najeriya mai shekara 26, mai suna Tomiwa Olaniyan, ya koka a shafin sa na Twitter, bayan ya yi asarar kuɗin mahaifiyarsa, N400k a caca.

A wani rubutu da ya yi wanda yanzu ya goge shi, Tomiwa wanda ya ke amfani da sunan @tomiwa201, ya roƙi wani mai siyar da littattafai, @Mrbankstips taimako, inda ya ce mahaifiyarsa tana buƙatar kuɗin domin siyan kaya saboda tafiyar da za ta yi ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel