Abun Al Ajabi
Wani mawaki dan Najeriya ya shiga jimami yayin da ya bayyana yadda aka watsa masa kudaden bogi bayan da ya watsa na gaske. An ga yana yayyaga kudaden nasa..
Aji Bukar Haziki matashi Ne mai Shekaru 15 a duniya ‘dan asalin jihar Borno wanda ya kera karamin Masallacin Ka’aba. Yaron mazaunin garin Maiduguri ne a Borno.
Bidiyon yadda manajan otal ya gaggauta hana saurayi shan lemonsa ya janyo cecekuce. Manajan Otal din ya ga budurwar ta CCTV tana yin barbade a lemon saurayin.
Wani matashi ya yanke shawarar goyo amaryarsa a kan babur zuwa wajen daurin aurensu inda bidiyon ya yadu a TikTok. Mutane sun ce hakan ya nuna soyayyar gaskiya.
Wani matashin yaro dake talla a titi ya ba jama’a Mamaki yayin da yake amsa tambayoyin lissafi tamkar na’ura mai kwakwalwa. Babu tabbacin yana zuwa makaranta.
Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno wata babbar mota cike da kudade yan naira dubu-dubu da aka fito da su daga wata jihar arewa, duk sun rube.
Wani ango da yaso birge amaryarsa tare da bayyana sabon salo wurin shiga wurin shagalin bikinsu ya bayyana a cikin akwatin gawa inda ya bar amarya baki bude.
Kasar Senegal ta yi yunkurin nemo malaman tsubbu domin yiwa Mane jinyar ciwon kafan da ya kamu dashi a wani wasan da ya bugawa Bayern Munich a cikin makon nan.
Wani mahaifi ya mutu yayin da ya umarci dansa ya gwada maganin bindiga a kansa. Wannan lamari ya haifar da hargitsi, hukumar 'yan sanda sun shiga. An kama dan.
Abun Al Ajabi
Samu kari