Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Za a Tashi Wasan Saudiya da Argentina 2:1 Awanni Kafin Wasan

Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Za a Tashi Wasan Saudiya da Argentina 2:1 Awanni Kafin Wasan

  • Wani dan Najeriya, Debo Popoola, ya yi hasashensa daidai yayin da ya wallafa a twitter cewa Saudiya zata doke Argentina a safiyar Talata, 22 ga watan Nuwamba
  • Don tabbatar da hasashensa, mutumin ya ce za a tashi wasa biyu da daya, cewa Saudiya zata kafa tarihi
  • Yan Najeriya da dama da suka ga wallafar da yayi na twitter game da gasar cin kofin na duniya sun nuna fushinsu cewa sun ga rubutun ne bayan ya tabbata

Wani dan Najeriya mai suna Debo Popoola, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da yayi hasashen yadda wasan kwallon kafa zata kasance tsakanin Saudiya da Argentina.

A wata wallafa da yayi a Twitter awanni kafin wasan, ya ce:

“Babban abun haushi a tarihin kwallon kafa zai faru a yau. Saudiya zata doke Argentina da ci 2 da 1."

Kara karanta wannan

Kungiyar Kwallon Manchester United Ta Raba Jiha Da Cristiano Ronaldo, Ba Zai Koma Old Trafford Ba

Yan Najeriya da dama basu ji dadin rashin ganin rubutunsa da wuri ba
Dan Najeriya Ya Yi Hasashen Za a Tashi Wasan Saudiya da Argentina 2:1 Awanni Kafin Wasan Hoto: @popsondebo, Sports Mole
Asali: Twitter

Hasashen mutumin ya yi daidai a wasan Saudiya da Argentina

Bayan an tashi wasan kamar yadda yayi hasashe, mutane da dama sun cika bangarensa na sharhi, suna fatan samu hasashe da dama a gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hirarsa da Legit.ng, Adebowale ya ambaci cewa wasan ba shine kadai abun da ya taba hasashe a kai ba. Yana mai cewa:

“Bana hasashen kwallon kafa. Amma na yi hasashen wasu abubuwa a baya. Ina ganin abu ne na hankali. Mutane da daman a da shi, amma muna bari ya gushe cike da kokwanto. Na daina yin caca kuma b azan koma ga haka ba.”

Kalli wallafarsa a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

@sch_fees17 ya ce:

"Dan Allah za ka iya fada mani kaddarata."

@moses_yhung ya ce

"Me yasa mutum baya ganin irin wadannan abubuwan da wuri ne."

Kara karanta wannan

Uban 'Yan Sa'a: Wani Mutumi Ya Taki Sa’a, Ya Ci Naira Tiriliyan 1 a Wajen Caca

@EfoEtornam ya ce:

"Wannan wallafar na bayyan ne bayan wasa."

@Lukxybea1 ya ce:

"Me yasa sai yanzu ne mutum ke ganin wannan."

@Pope_alorgy ya ce:

"Ba zaka taba ganin wannan hasashen ba sai bayan an gama wasa."

@Nedu_bangz ya tambaya:

"Dan Allah shin OBI ya lashe zaben 2023?"

A wani labarin kuma, mun ji cewa Sarkin Saudiyya, Sarki Salman, ya baiwa al’ummar Kasarsa hutu ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba bayan lallasa Argentina da yan wasan kasarsa suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel