Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya

Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyoyin wani magidanci da ya auri doguwar mace
  • Matar mai shekaru 27 mai suna Elisane Silva ta auri burin ranta Francinaldo Da Silva Carvalho a 2015
  • Matar wacce ta rungumi baiwar da Allah ya yi mata tare da toshe kunnuwanta daga sauraron duk wani kushe tana da mabiya fiye da miliyan 3 a TikTok

Brazil - Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyoyin wata kyakkyawar mata mai shekaru 27 wacce Allah ya yiwa baiwar tsawo.

Tsawon matar mai suna Elisane Silva daga Salinopolis a kasar Brazil, ya kai kimanin sahu 6 da inci 8.

Iyali
Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya Hoto: TikTok/@elisane_oficial
Asali: UGC

Tun bayan da ta auri masoyinta Francinaldo Da Silva Carvalho a 2015, matar ta yi biris da suka da ba a da ake mata saboda tsawonta inda ta zama fitacciya a shafukan yanar gizo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Shafinta na TikTok mai suna @elisane_oficial na da mabiya fiye da miliyan 3.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A shafukan soshiyal midiya, ta kan kayatar da jama’a da kyawawan hotunansu tare da mijinta da yaransu.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Jama'a sun yi martani

Datu Wilborne Sangha ya ce:

"Kyawunta saukakke ne, za ki iya zama kawata?dan Allah....Ni yar Philippines ce."

ThessSpirit ta ce:

"Kyakkyawar yarinya mai tsawo sosai.
"Kuma karamin na da kyau da jinjirar."

JohnSabai ya ce:

"Dan Allah ki je Amurka ki buga wasan jefa kwallo a raga...shakka babu za ki zama tauraruwa."

Hillary KingLarry ta ce:

"Za ki yi daidai da wasan jefa kwallo a raga."

'Saurayina Ya KomaTurai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena': Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta je shafin TikTok don bayyana yadda saurayinta ya koma Turai da zama mako daya bayan ya nemi auranta.

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Soki Mijinta Da Wuka Har Lahira Kan Ya Nemi Hada Shimfida Da Ita

A wani bidiyo, budurwar mai suna zaynab_azeez a TikTok ta bayyana cewa mutanen da suka san da naman auren suna ta yi mata ba’a tare da hasashen cewa wata kila soyayyarsu ta bi ruwa.

Ta bayyana cewa yan watanni kadan bayan nan, sai mutumin ya dawo Najeriya sannan ya aure ta. Wani bangare na bidiyon ya haskota rike da takardar shaidar aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel