Magidanci Ya Ci Cacar N13bn, Ya Boyewa Matarsa da ‘Dansa 1 Tilo

Magidanci Ya Ci Cacar N13bn, Ya Boyewa Matarsa da ‘Dansa 1 Tilo

  • Wani mutum ‘dan asalin Kudancin Chana ya ci 219 miliyan Yuan a caca wacce tayi daidai da N13 biliyan kuma ya boye wannan ya zama sirrinsa.
  • Mutumin yayi ikirarin cewa bai bayyanawa iyalansa wannan sa’a da ya taka ba saboda tsoron kada kudin sun canza musu dabi’arsu
  • Ya sadaukar da wani bangare na kudin mai tarin yawa ga mabukata kuma har a halin yanzu bai riga ya yanke hukuncin abinda zai yi da sauran kudin ba

Mutane da yawa idan suka samu makuden kudi, abu na farko da zasu fara yi shi ne kyautatawa tare da barakasa ga wadanda suke kauna.

Mista Li
Magidanci Ya Ci Cacar N13bn, Ya Boyewa Matarsa da ‘Dansa 1 Tilo. Hoto daga Timesnews.co.za
Asali: UGC

Yayin da wani mutum ‘dan asalin kasar Chana a kudancinta yayi nasarar samun lashe cacar 219 miliyan Yuan wanda yayi daidai da N13 biliyan, shi bai yi yadda kowa ke yi ba.

Kara karanta wannan

Sababbin kudi: EFCC da ICPC Za Su Sa Ido Kan Masu Cire Makudan Kudi Inji CBN

Sau da yawa jama’a dake da tarbiya mai kyau idan sun samu kudi, su kan rude tare da shiga ribibi inda suke karewa wurin barnatar da kudin kan abubuwan da basu dace ba, hakan kuwa za a ce kusan duk wanda ya wahala ya samu kudinsa yake tsoro.

Times Live ta rahoto cewa, mutumin mai suna Li, ya yi shiru bai bayyanawa kowa samunsa ba ta yadda iyalansa zasu cigaba da aiki tukuru tare da jin dadin duk abinda suka samu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilinsa na boyewa matarsa da ‘dansa

“Ban fadawa matata da ‘da na ba saboda tsoron cewa zasu canza kuma ba zasu yi aiki tukuru ba ko a nan gaba.”

- Mutumin ya bayyanawa jaridu.

A matsayinsa na mutum maras girman kai da hali nagari, Li ya sadaukar da yuan miliyan 5 wanda yayi daidai da N310 miliyan ga mabukata, kuma ya adana sauran har yanzu bai san abinda zai yi dasu ba.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Wani mutum ya ci cacar N413m, an bashi zabi

A wani labari na daban, wani magidanci ya taki sa’a da sassafe bayan ya fita siyawa yaransa madara da alawa a Amurka.

Ya yanke shawarar gwada wata caca inda a kan take ya ci kudin da suka kai $1m wanda ya haura N413m a watan Disamban 2021.

A tarihi, Dennis ne mutum na 2 d aka taba lashe cacar kuma ya bukaci kashi 30 kacal daga ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel