Masu Tsaron Gabar Ruwan Spain sun Kama ‘Yan Najeriya 3 da Suka Makale a Kasan Jirgi

Masu Tsaron Gabar Ruwan Spain sun Kama ‘Yan Najeriya 3 da Suka Makale a Kasan Jirgi

  • Sojojin dake tsaron gabar ruwan kasar Spain sun gano wasu mutum uku da suka makale ta kasan jirgin ruwa daga Najeriya har zuwa tsibirin Canary
  • Mutane uku wadanda duka maza ne, sun bi jirgin da ya dauka man fetur daga Legas a Najeriya har zuwa kasar inda suka yi kwanaki 11 suna tafe
  • An gaggauta mika su asibiti sakamakon rashin ruwan da suke fama da shi a jikinsu bayan bin jirgin Althini II da ya tashi daga Legas

Masu tsaron gabar ruwa na kasar Spain sun ce sun ceto mutum uku ‘yan gudun hijira da suka boye a wani sako na jirgin ruwa da ya isa tsibirin Canary daga Najeriya.

Masu gudun hijira
Masu Tsaron Gabar Ruwan Spain sun Kama ‘Yan Najeriya 3 da Suka Makale a Kasan Jirgi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana, masu tsaron gabar ruwan sun sanar da hakan ne a Twitter a ranar Litinin.

Wallafar ta hada da mutum ukun da suka boye a ta kasan jirgin ruwan da ya dauka mai da kemikal.

Jirgin Althini II din ya isa Las Palmas a Gran Canaria a ranar Litinin bayan kwashe kwanaki 11 da yayi yana tafiya daga Legas, Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

TheCable ta rahoto cewa, bayan gano su, masu gudun hijiran an kwashesu an mika su asibiti tare da magance musu matsalar rashin ruwan da ta addabesu.

Har yanzu dai ba a tabbatar da cewa mazan uku sun kwashe wannan tsawon lokacin bane a makale a sakon jirgin ruwan.

Tsibirin Canary din mallakin kasar Spain ne kuma fitacciyar hanya ce da masu gudun hijira daga Afrika ke bi domin isa Turai.

Kamar yadda kiyasin Spain ya bayyana, gudun hijira ta ruwa ya kai kashi 51 a cikin watanni biyar na farkon shekarar nan inda aka gwada da shekarar da ta gabata.

Lamarin nan na zuwa ne kasa da mako daya bayan Kungiyar masu gudun hijira na duniya tayi ikirarin cewa a kalla mutum 50,000 ne suka rasa rayukansu a kokarinsu na samun ingantacciyar rayuwa tun daga 2014, Reuters ta rahoto.

IOM ta rahoto cewa kasashen Afrika ne ke da kashi mafi yawa inda sama da mace-mace 9,000 aka samu a hanyoyi masu hatsari Kamar su Sahara da tekun Mediterranean.

Yaro Maraya ya boye a jirgin sama

A wani labari na daban, an Tsinta wani yaro mai shekaru 14 wanda aka gano maraya ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Legas.

Yaron ya makale a fiffiken jirgin sama inda yace ya gaji da Najeriya baki daya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel