“Shekaru 3 Kenan Da Na Fara Tuyan Kosai”: Matashiya Ta Yi Murna a Bidiyo, Jama’a Sun Jinjina Mata

“Shekaru 3 Kenan Da Na Fara Tuyan Kosai”: Matashiya Ta Yi Murna a Bidiyo, Jama’a Sun Jinjina Mata

  • Wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya ta ba da labarinta yayin da take bikin cika shekaru uku da fara tuyan kosai.
  • A wani bidiyo da ta wallafa a Instagram, ta bayyana yadda ta ke fadi tashi tare da hada neman kudi da karatu
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjina mata kan yadda ta dukufa wajen ganin ta cimma nasara a rayuwa

Wata kyakkyawar daliba yar Najeriya mai suna Amaka wacce ke sana’ar tuya kosai, ta burge mutane da dama bayan ta bayar da labarin rayuwarta.

A wani dan gajeren bidiyo, budurwar ta bayyana yadda ta hada karatu da sana’a sannan ta mika godiya ga Allaha kan yadda ya saka mata hannu a lamuranta.

Budurwa a bakin sana'a
“Shekaru 3 Kenan Da Na Fara Tuyan Kosai”: Matashiya Ta Yi Murna a Bidiyo, Jama’a Sun Jinjina Mata Hoto: @datswatzup
Asali: Instagram

Kalamanta:

“A ranar 20 ga watan Nuwamban 2019, na fara sana’ar siyar da kosaina. Na samu gurbin karatu a wannan shekarar. Ba abu mai sauki bane hada karatu da sana’a. Wata rana hatsari ya afku a shagona amma nagode Allah ban bude ba a wannan rana. Bani da lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wasu lokutan na kan zurfafa a tunani saboda ina ganin ban yiwa kaina abubuwan da ya kamata. Wasu lokutan na ji babu dadi sannan na sha kuka na. Ina ta gwagwarmaya duk runtsi duk wuya. Duk zafin rana. Wasu lokutan a cikin ruwan sama.
“Na ci gaba da sana’ata cikin farin ciki. Na fara haske. Ban taba danasanin daukar wannan matakin ba daidai da rana daya. Yanzu ina matakin karatu na uku a jami’a. Shekara daya yayi mun saura. Ina taya kaina murnar cika shekaru uku. Yau shekaru uku daidai da na fara tuyar kosai.”

Amaka ta magantu kan abun da ya karfafa mata gwiwa

Da aka tambayeta game da abun da ya karfafa ta, Amaka ta fadama Legit.ng cewa:

“Lokacin da baka da wani da ke baka da kashe maka kudi, baka da wani zabi da ya wuce ci gaba da gwagwarmaya sai dai idan kana so ka sa-dakar gaba daya.”

Jama’a sun jinjinawa mai tuyan kosan

Oluwaseungreatness ta ce:

“Ki ci gaba yarinya. Allah zai albarkaci nemanki sannan ya aiko da tallafi gareki da sunan Yesu.”

Cullinan_vintage_lifestyle ta rubuta:

“Ki tsaya tsayin daka yar kasuwa! Wannan ya daukaka ni, har yanzu akwai mata nagari.”

Miszchakkie ta rubuta:

“Allah ne zai sakawa kokarinki da nasara. Ki ci gaba.”

Lauryella ta yi martani:

“Irin wadannan matan ne suka cancanci tallafi na gaske.”

Kalli bidiyon a kasa:

Manoman kwai na gab da rufe aiki saboda tsadar abincin kaji

A wani labari na daban, hasashe sun nuna manoman kwai sun gaji da yadda farashin abincin kaji ke ta tashin gwauron zabi domin dai sun fara tunanin hakura da sana'ar.

An yi ittifakan idan har ba a samu mafita ba abun zai yi matukar tasiri a kan yan Najeriya domin dai za a samu karancin kwai kuma yan kadan da za su rage za su yi tsada matuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel