Budurwa Ta Saki Bidiyon Saurayinta Da ke Siyar Da Kosai, Ta Caccaki Masu Soyayya Da Yan Yahoo

Budurwa Ta Saki Bidiyon Saurayinta Da ke Siyar Da Kosai, Ta Caccaki Masu Soyayya Da Yan Yahoo

  • Wata matashiya yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don nuna saurayinta wanda ke soya kosan siyarwa
  • Da take hoton selfie da shi yayin da yake bakin sana’arsa, budurwar ta caccaki yan mata da ke soyayya da yan damfara
  • A cewarta, lamarinsu ya fi na mutanen da ke soyayya da yan yahoo wadanda suka dogara da damfarar mutane

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin saurayinta wanda ke sana’ar soya kosai.

A wani bidiyon TikTok, budurwar ta nuna matashin wanda ke gudanar da harkokin kasuwancinsa sannan ta aika sako ga mutanen da ke soyayya da yan yahoo.

Saurayi da budurwa
Budurwa Ta Saki Bidiyon Saurayinta Da ke Siyar Da Kosai, Ta Caccaki Masu Soyayya Da Yan Yahoo Hoto: TikTok/@official_caro2
Asali: UGC

Ta ce rayuwar saurayinta ya fiye mata sau dubu domin dai basu dogara da aikata laifuka don samun na sakawa a baki ba.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Murna Yayin da Ta Cika Shekaru 3 Da Fara Sana’ar Soya Kosai, Bidiyon Ya Yadu

“Kuna gani ko, ku ga saurayina. Kosai yake siyarwa,” cewarta yayin da take bidiyo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mutanen da ke soyayya da yan yahoo, a duk lokacin da ya kama za ku ci. Idan bai kama ba za ku dogara ga Allah…”

Mutane da dama sun ji dadin yadda take kaunar saurayin nata saboda Allah inda suka yi masu addu’a samun wadata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Cele/BTC ta ce:

“Fada mana gaskiya cewa bas hi kadai kike soyayya da shi ba. Ban zo da fada ba.”

kingsb126 ya ce:

“Allah Ubangiji ya wadata ku…Ci gaba da gashi dan uwa.”

KÏÑG TÁÏWØ ya ce:

“Kada ka kula su dan uwa idan dai kana samun kudin siyan abinci ka fi karfin komai kuma ka auri yarinyar nan faaaa.”

RawGermRex01 ya ce:

“Allah ya albarkace ki da baki kaskanta shi ba da kuma jin kunyar soyayya da shi.”

Kara karanta wannan

Kaddara Ta Riga Fata: Kyakkyawar Budurwa Ta Kaso Aurenta Bayan Watanni 3, Ta Wallafa Hotunan Shagalin Bikin, Jama’a Sun Yi Martani

Budurwa ta kama sana'ar kosai don dogaro da kai

A gefe guda, mun ji cewa jama'a a soshiyal midiya sun jinjinawa wata budurwa bayan ta kama sana'ar siyar da kosai domin daukar dawainiyar kanta da na karatunta.

Matashiyar mai suna Amaka tana lebel 300 a jami'a amma kuma hakan bai hana ta gudanar da sana'arta ba duk rintsi duk wuya. Shekararta uku kenan da fara wannan sana'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel