An Tsinci Gawar Budurwa ’Yar Jihar Bayelsa a Cikin Durowan Kaya a Otal
- An gano gawar wata yarinya mai shekaru 16 a dakin otal, lamarin da ya jawo cece-kuce da jimami a yankin jihar Bayelsa
- 'Yan sanda na ci gaba da bincike don gano musabbabin mutuwar yarinyar da aka gano a cikin wata durowar dakin otal
- A bangare guda, an tsinci gawar wasu mutane biyu da suka mutu a wani daki a jihar Bauchi, an shiga firgici
Brass, jihar Bayelsa - An tsinci gawar wata yarinya 'yar shekaru 16 mai suna Nengi Enenimiete a cikin durowar kaya a dakin otal a tsibirin Twon-Brass a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, masu shara ne a otal din suka gano gawar wacce tuni ta fara rubewa, ta fara wari.
An ce mutumin da suka shigo dakin tare da yarinyar tuni ya fita a otal din bayan wani lokaci.
A cewar majiya daga otal din, babu alamar rauni ko wata tsangwama a jikin gawar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mazauna yankin Brass tuni suka tada bore tare da bayyana bukatar a yi gwajin gawa don gano wanda ya kashe ta tare da daukar mataki.
Farkon yadda lamarin ya faru
A cewar bincike, kawar marigayiyar ce ta gabatar da ita ga wani bako a ranar Asabar, inda su biyun suka kama dakin otal a daren da nufin fita a ranar Lahadi.
Majiya ta shaida cewa, yayin da manajan otal din ya zo bincika dakin bayan fitan wanda ya kama, ya ga ko'ina a birkice, take ya umarci masu shara su gaggauta share dakin.
Amma yayin da aka fara sharan, sai aka ga ruwa na fita daga wani bangare na dakin, musamman ta jikin durowar.
A cewar majiyar:
"Yayin da suke duba dakin, sun ji matsanancin wari, sai kuma aka fara duba daga ina ne warin. Daga baya suka gano gangan jikin mutum ba ta motsi a cikin durowar."
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an dauki gawar zuwa asibiti domin ci gaba da bincike, haka nan Tribune Online ta ruwaito.
Butswat ya ce, ya zuwa yanzu ana bincika musabbabin mutuwar da kuma kokarin gano wanda ya aikata kisan ita ya tabbata laifin kisa ne.
Yanayi irin wannan mai cike da tashin hankali ya faru a jihar Bauchi, inda jami'an tsaro suka bankado wasu gawarwaki a wani gida.
Asali: Legit.ng