Uwa Ta Yi rawan Murna Yayin da Saurayin Diyarta Ya Kama Masu Gidan Haya, Ya Mayar Da Su Yan Gayu

Uwa Ta Yi rawan Murna Yayin da Saurayin Diyarta Ya Kama Masu Gidan Haya, Ya Mayar Da Su Yan Gayu

  • Wani matashi dan Najeriya ya sha ruwan yabo bayan ya kamawa iyayen budurwarsa gidan haya mai kyau
  • Mahaifiyar budurwar ta cika da farin ciki da wannan babban kyauta inda ta dungi rawa tana zagaye gidan wanda babu komai ciki don nuna godiyarta
  • Yan Najeriya da suka yi martani ga bidiyon sun ce karamcin da matashin ya yiwa dangin budurwar tasa ya taba zukatansu sosai

Wani matashi dan Najeriya mai suna @infoxpressblog1, wanda ke yin bidiyoyi a kan soyayyarsa a TikTok, ya nuna yadda ya sanya iyayen budurwarsa farin ciki.

A wani bidiyo da ya saki a baya, matashin ya nunawa mutane irin gidan da budurwar da iyayenta ke zama wanda bai da kyan gani.

Yan uwan budurwar durkushe suna murna
Uwa Ta Yi rawan Murna Yayin da Saurayin Diyarta Ya Kama Masu Gidan Haya, Ya Mayar Da Su Yan Gayu Hoto: TikTok/@infoxpressblog1
Asali: UGC

Dan Najeriya ya karbarwa dangin budurwarsa hayar gidan yan gayu

A ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba, matashin ya dauki bidiyon lokacin da ya kai mahaifiyar budurwar tasa gidan yan gayu da ya karbar masu haya. Yana ta zullumin ko matar zata so gidan.

Kara karanta wannan

Zai yiwu kuwa? Dan Najeriya ya ba da labarin yadda ya mutu kana ya dawo duniya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lokacin da matar ta bude kofar gidan sannan ta gan shi dauke da shafe na zamani, sai ta daka tsalle cike da farin ciki yayin da take godiya ga Allah a kan wannan ni’ima da yayi masu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani masu tsima zuciya

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu martani kusan 10,000 da ‘likes’ fiye da 200,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

‘Electricfunds ta ce:

“Ina ji kamar nayi kuka.. yanzu na fahimci wannan maganar..kada ki auri mai kudi maimakon haka ki auri mai bayarwa.”

Daniel Stanley ya ce:

“Ina yin kujeru dan uwa. Idan kana bukatar a kawata shi zai yi aikin kyauta, kawai ka siya mun kayan aiki.”

sandraojemekele Kiki ta ce:

“Wannan ya sa hawaye zuba a idanuna…dan Allah wani ya danna ‘like’ don na dunga dawowa.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tona sirrin gwamnoni, ya ce ba zai yi Allah wadai da wata kasurgumar kungiyar ta'addanci ba

dhammie35 ya ce:

“Idan yarinyar nan bata auri yaron nan ba a karshe…musamman ni zan wanketa soso da sabulu.”

Bernard Kwame Ayimah ta ce:

“Ita din uwa ce mai godiya da abun da Allah ya raba ya bata. Allah ya bata tsawon rai sannan ya albarkaci ayyukan hannunta.”

Babban yaro ya ja hankalin yan jami'a

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi ya tashi kan yan maza da mata a jami'ar Lagas bayan ya isa makarantar a cikin wata dankareriyar mota.

Motar tasa kirar wanda farashinta ya kai naira miliyan 24 ta matukar jan hankalin jama'a inda suka zagayeta tare da saka albarka ta hanyar tabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel