Bola Tinubu
Mun kawo labarin inda aka kwana game da alkawarin raba kayan abinci saboda ana yunwa. An tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa talakawa.
A game da tashin Dala, wani masani ya haska kuskuren gwamnatin Bola Tinubu. IMF ta ce $1 za ta haura N2000 a 2024, masanin ya taba ba Muhammadu Buhari shawara.
Bayan gudanar da sahihin bincike, Legit Hausa ta gano cewa ba Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ne ya muzanta matar Tinubu a bidiyo ba sabanin rahoton Vanguard.
Shehu Sani ya yi Allah wadai da kiran da Malamin Musulunci ya yi na neman a kasha matar Shugaban kasa Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu. Ya ce ba abun yarda bane.
Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta amince da rabawa manoma takin zamani tare da kuma kaddamar da dakarun gona don yaƙi da 'yan ta'adda da ke farmakar manoma.
Harkokin kasuwanci sun tsaya caka Legas yayin da wani mutum ya rasa ransa da wasu suka jikkata bayan an kare tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar.
Yayin da ake cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa a Najeriya, hukumar Kwastam ta fara raba kayan abincin da ta kwace a yau Juma'a 23 ga watan Faburairu.
Alamu masu karfi na nuni da cewa kungiyar ECOWAS za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar biyo bayan sauyin gwamnati a kasashen uku.
Bola Tinubu ya bukaci al’umma su cire rai da zancen maido tsare-tsaren da aka saba da su. Janye tsarin tallafin fetur da karya Naira ne suka jefa mutane a wahala.
Bola Tinubu
Samu kari