Kwanaki 3 Bayan Nasarar Kwankwaso a Kotu, Uban NNPP Ya Nemi Hadin Kai Kan Abu 1 Game da Tinubu

Kwanaki 3 Bayan Nasarar Kwankwaso a Kotu, Uban NNPP Ya Nemi Hadin Kai Kan Abu 1 Game da Tinubu

  • Kwanaki kadan bayan Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi nasara a kotu kan korarsa, jigon NNPP ya nemi hadin kan ‘yan kasa
  • Uban jam’iyyar ta kasa, Dakta Boniface Aniebonam ya ce a yanzu ba lokacin zage-zage ba ne a gwamnatance sai dai hadin kai
  • Aniebonam ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Faburairu a jihar Legas inda ya ce Tinubu na bukatar addu;ar don ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Dakta Boniface Aniebonam, uban jam’iyyar NNPP ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Boniface ya ce yanzu ba lokacin kushe-kushe ba ne da zargin juna ya kamata a yi hakuri da mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

NNPPta bukaci hadin kai da addu'a ga Tinubu don samun ci gaba
Jam'iyyar NNPP ta bukaci addu'o;i ga Tinubu don fita daga matsalar kasar. Hoto: Rabiu Kwankwaso, Bola Tinubu, Boniface Aniebonam.
Asali: Facebook

Menene uban jami'yyar NNPP ke cewa?

Aniebonam ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Faburairu a jihar Legas inda ya ce Tinubu na bukatar addu'a;ar don ci gaba, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Bari mu fadi wannan ga ‘yan Najeriya, dole ne a matsayinmu na ‘yan kasa mu goyawa Bola Tinubu baya don dakile matsalolinmu.
“Ana daukar wadannan tsauraran matakai ne a Najeriya don tabbatar da cewa an samu abin da ake nema.
“Shugaba Tinubu duk da haka ya na da kwarin gwiwa ganin halin da ake ciki yanzu inda ya ce ba za a samu ci gaba ba sai da bin doka.”

Uban jam’iyyar ya ce ya na yiwa shugaban fatan nasara da kuma dakile matsalolin kasar inda ya ce Najeriya za ta sake zama giwar Afirka.

Nasarar Kwankwaso a kotu

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Uban jam’iyyar ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan jigon jam’iyyar, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi nasara a kotu.

Kwankwaso ya garzaya kotun ne don kalubalantar umarnin kora da jam’iyyar ta aike masa kan wasu zarghe-zarge.

A cikin wata sanarwa da ta sake fitarwa a kwanakin baya, NNPP ta ce har zuwa lokacin Kwankwaso ba dan jam’iyyar ba ne.

Daga bisani kotun ta yi fatali da matakin da jam’iyyar ta dauka inda ta ce Kwankwaso cikakken dan jam’iyya ne.

Ganduje ya rasa jiga-jigan APC

A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC, Umar Ganduje ya tafka asara yayin da wasu jiga-jigai suka balle.

Ciyamomin kananan hukumomi uku ne a jihar Kano suka koma NNPP daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel