Meye Gaskiyar Batun CAN Ta Nemi a Hukunta Sheikh Dutsen Tanshi Kan Bantanci Ga Remi Tinubu?

Meye Gaskiyar Batun CAN Ta Nemi a Hukunta Sheikh Dutsen Tanshi Kan Bantanci Ga Remi Tinubu?

  • Bayan gudanar da sahihin bincike, Legit Hausa ta gano cewa ba Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ne ya muzanta matar Tinubu a bidiyo ba
  • Jaridar Vanguard ce ta fara ruwaito cewa Sheikh Abdulaziz ne ya nemi Musulmi su kashe Remi Tinubu saboda kasancewar ta 'kafira'
  • Sai dai a binciken da Legit ta yi, ta gano cewa ba Abdulaziz ba ne a cikin bidoyon ba, kuma kungiyar CAN ba ta nemi a kama malamin na jihar Bauchi ba

Bidiyon wani malamin addinin Muslunci yana zafafa suka a kan gwamnatin Shugaba Tinubu ya bar baya da kura, inda aka ji malamin na neman a kashe Remi Tinubu saboda 'kafira' ce.

Bayan ɓullar wannan bidiyon, jaridar Vanguard ta wallafa labari mai taken: "Remi Tinubu: Matasan ƙungiyar CAN sun nemi a kama tare da hukunta Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi."

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Ba Sheikh Dutsen Tanshi ne ya yi kalaman bantanci ga Remi Tinubu ba
Ba Sheikh Dutsen Tanshi ne ya yi kalaman bantanci ga Remi Tinubu ba - Binciken Legit.
Asali: Twitter

Jaridar ta ce Sheikh Abdulaziz ne malamin da ke jawabi a bidiyon, kuma shi ne ya ce a kashe Remi Tinubu, wanda ya harzuka matasan kungiyar CAN.

A cikin wata sanarwa da jaridar ta ce kungiyar CAN ta fitar, matasan sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki kan Sheikh Abdulaziz.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga ina batun ya fara fitowa?

A binciken da Legit Hausa ta gudanar, ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu ne bidiyon malamin ya fara karaɗe kafofin sada zumunta, wanda ya jawo cece kuce.

Wani ma'abocin shafin X, Lawrence I. Okoro ya wallafa bidiyon malamin wanda ya yi kakkausar sukar ga gwamnatin Tinubu tare da cewa "ya kamata a kashe ta saboda kafira ce."

A cikin bidiyon, malamin ya yi ikirarin cewa yaudarar 'yan Najeriya APC ta yi a zaben 2023 inda ta ce a zabi shugaban kasa da mataki duka Musulmai.

Kara karanta wannan

"Ban san me ya hau kaina ba": Matashi ya sheke mahaifiyarsa, ya kona gidansu

Kalli bidiyon a kasa:

Ikirarin da jaridar Vanguard ta yi

Bayan nazarin wannan bidiyon, Legit Hausa ta gano cewa ikirarin da jaridar Vanguard ta yi na cewa malamin Sheikh Idris Abdulaziz ne ƙarya ce tsagwaronta.

Kamannin malamin da ke a jikin bidiyon sam ba na Sheikh Abdulaziz ba ne, sabanin yadda Vanguard ta ɗora alhakin dukkan kalaman akan Abdulaziz.

Jaridar ta kuma ce matasan kungiyar CAN sun fitar da sanarwar a kama Sheikh Abdulaziz, amma iya binciken Legit, ba ta ga wata sanarwa daga shafin kungiyar matasan ba.

Hujjojin da suka bayyana akan wannan lamari

Da farko dai, bidiyo ya nuna karara cewa malamin da ya kalaman batancin ba Sheikh Abdulaziz ba ne, ba kuma muryarsa ba ce.

Matasan kungiyar CAN ba su fitar da wata sanarwa ta a kama Sheikh Abdulaziz ba, domin babu wannan sanarwar a duk kafafen watsa labarai.

Vanguard ce kadai jaridar da ta wallafa cewa Sheikh Idris Abdulaziz ne malamin da ya yi kalaman, wanda ya nuna akwai rauni a zargin.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Hukuncin karshe: Gaskiyar abin da ya faru

Har zuwa lokacin da Legit Hausa ta tattaro wannan bayani, ba ta iya tantance malamin da ke a jikin bidoyon ba, amma ta tabbatar da cewa ba Sheikh Idris Abdulaziz ba ne.

Legit Hausa ta gane cewa labarin jaridar ƙanzon kurege ne kawai, wanda za a iya kira da 'ƙazafi' ga malamin ɗan asalin jihar Bauchi.

Duk wanda ya ci karo da rahoton Vanguard na cewa kungiyar CAN ta sa a kama Sheikh Abdulaziz, to ya sani labarin ba shi da inganci, domin ba shi da makama balle tushe.

Abin da Shehu Sani ya ce game da kalaman malamin

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da kalaman malamin da ya nemi a kashe Remi Tinubu saboda kawai ita Kirista ce.

Sani ya ce sukar gwamnati da manufofinta abu ne da 'yancin dimokuraɗiyyar kasar ya ba da dama, amma neman a kashe mutum wani abu ne da ba za a amince da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel