Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Malamin Musulunci Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu

Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Malamin Musulunci Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu

  • Shehu Sani ya yi Allah wadai da furucin da wani malamin Musulunci ya yi kan matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu
  • Sani ya jaddada cewar kiran da malamin ya yi na a kashe Sanata Remi Tinubu ba abun yarda bane kuma ya kamata a yi Allah wadai da shi
  • Da suke martani ga furucin Sani a shafinsa na soshiyal midiya, 'yan Najeriya da dama sun bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta kama malamin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi martani bayan wani malamin addinin Musulunci ya ayyana cewa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta cancanci mutuwa saboda kasancewarta fasto.

Sani ya yi Allah wadai da furucin malamin sannan ya jaddada cewar 'yan kasa na da 'yancin sukar gwamnati da manufofinta, amma neman mutuwar matar shugaban kasar ba abun yarda bane.

Kara karanta wannan

Matakin Tinubu 1 ya jefa Najeriya cikin wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

Sani ya yi watsi da neman a kashe Remi Tinubu
Shehu Sani Ya Magantu Yayin da Malamin Musulunci Ya Nemi a Kashe Matar Tinubu Hoto: Senator Shehu Sani, SEN. OLUREMI TINUBU, CON
Asali: Facebook

A wani bidiyo da ya yadu, wanda aka wallafa a shafin X a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, an jiyo wani malamin addini yana cewa tikitin Musulmi da Musulmi da ya kawo Tinubu mulki duk yaudara ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SaharaReporters ta tabbatar da cewa malamin, wanda Legit.ng ta kasa tantance ko wanene shi a lokacin wannan rahoto, ya ce matar shugaban kasa, “kasancewar ta kafiri ya kamata a kashe ta kamar yadda Alkur’ani ya tanada."

Sai dai bai bayar da wata sura ko ayar Alqur’ani da za ta marawa ikirarin nasa baya ba.

"Yanzu, Tinubu @officialABAT, matarsa kafira ce. Duk da kasancewarta kafira, ita din babba ce a cikin kafirai. Hatta da ita, hukuncin Allah ya ce dole a kashe ta...Fasto ce ita...Shugabar kafirai, Allah ya ce dole a kashe su," inji malamin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zakzaky yana magana kan harsashi 38 da likitoci suka gano a kwakwalwarsa ya yadu

Shehu Sani ya yi Allah wadai da kalaman malamin

Da yake martani, Shehu Sani a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, ya caccaki maganganun malamin.

Sani ya ce:

"Sukar gwamnati da manufofinta yana cikin tsarin 'yancin dimokradiyya; amma neman a kashe Sanata Remi Tinubu da malamin addinin ya yi abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin Allah wadai ne."

Kalli bidiyon malamin da ya ce a kashe matar Tinubu a kasa:

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wasu Musulman 'yan Najeriya kan kira da malami ya yi na neman a kashe matar shugaban kasar.

Malama Khadija ta ce:

"Gaskiya wannan abu da malamin ya yi ba daidai bane kuma bai kyauta ba. Ko Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wassalam wanda da shine muke koyi ya zauna lafiya da kafirai a lokacinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi zancen mayar da tallafi da soke karya naira saboda shiga kuncin rayuwa

"Kamata ya yi a dunga tafiyar da addini ba tare da gaba ko son zuciya ba. Kira da malamin nan ya yi abun Allah wadai ne kuma irin haka ne yake haifar da tarzoma da kiyayya a tsakanin al'umma."

Malam Nuraddeen kuwa cewa ya yi:

"Ya kamata mahukunta su dauki mataki kan irin wadannan malamai masu yada kiyayya a tsakanin al'umma. Me ma zai sa ka ce a kashe mutum ba tare da ya aikata wani laifi ba? Koda laifi mutum ya yi ai akwai hukuma wadanda sune ke da hurumin yanke hukunci.
"A matsayina na Musulmi kuma 'dan Najeriya ina yin tir da abin da malamin nan ya yi kuma ya kamata ya gaggauta janye maganarsa ko don a samu zaman lafiya a tsakanin al'ummar kasar."

Shehu Sani ya caccaki sarakunan Arewa

A wani labarin, mun ji cewa Shehu Sani, ya yi Allah wadai da sukar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Tinubu da sarakunan Arewa ke yi saboda matsin rayuwar da 'yan Najeriya ke fuskanta.

Legit Hausa ta rahoto a baya cewa shugaban, majalisar sarakunan gargajiya na Arewa kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya ce Najeriya na dane ne kan bam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel