Gowon Ya Sasanta Rikicin ECOWAS da Nijar, Mali da Burkina Faso, Za a Janye Masu Takunkumi

Gowon Ya Sasanta Rikicin ECOWAS da Nijar, Mali da Burkina Faso, Za a Janye Masu Takunkumi

  • Rahotanni na nuni da cewa kungiyar ECOWAS za ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙabawa Mali, Nijar da Burkina Faso
  • Wannan ya biyo bayan wasikar da Yakubu Gowon ya aika wa shugabannin ECOWAS na hanyoyin magance matsalolin kasashen uku
  • A baya-bayan nan kasashen uku suka fice daga kungiyar tare da sanar da shirinsu na kafa tarayyar kasashen su mai zaman kanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Alamu masu karfi na nuni da cewa kungiyar ECOWAS za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar biyo bayan sauyin gwamnati da aka yi a kasashen uku.

Wasu majiyoyi da dama sun shaida wa Daily Trust a ranar Alhamis cewa, matakin zai hana kasashen uku cimma burinsu na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.

Kara karanta wannan

Sabuwar annoba ta kashe ma’aikatan lafiya uku da marar lafiya a asibitin sojin Najeriya

ECOWAS na duba yiwuwar dage takuntukumi akan Nijar, Mali da Burkina Faso.
ECOWAS na duba yiwuwar dage takuntukumi akan Nijar, Mali da Burkina Faso. Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Abin da ya jawo sabanin kasashen da ECOWAS

Vanguard ta ruwaito cewa ministocin kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar a ranar Alhamis 15 ga watan Fabrairu sun bayyana shirin kafa kungiyar tarayyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Janairun bana ne kasashen uku suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS, kungiyar da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

An bukaci su sake tunani, bisa dalilai daban-daban, ciki har da wahalhalun da jama'arsu za su iya fuskanta.

Shawarar da Yakubu Gowon ya ba wa ECOWAS

Sai dai wasu majiyoyi sun ce hukuncin da gwamnatocin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka dauka ya haifar da abin kunya ga kungiyar ECOWAS.

A ranar Laraba, tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, ya yi kira ga ECOWAS da ta dage dukkan takunkumin da ta kakaba wa kasashen uku.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Yayin da ya nuna muhimmancin kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, ya kuma yi kira garesu da su janye sanarwarsu na ficewa daga kungiyar ECOWAS.

ECOWAS za ta duba yiwuwar dage takuntumi

Gowon, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar ECOWAS, ya yi wannan kiran ne a wasikar da ya aike wa Dr. Omar Alieu Touray, shugaban hukumar ta ECOWAS a ranar Laraba a Abuja.

Da yake karbar wasikar, shugaban hukumar ECOWAS, ya tabbatar wa dattijon cewa zai aika da wasikar ga daukacin shugabannin kasashen ECOWAS.

"A ranar Asabar ne aka shirya gudanar da wani babban taro na ECOWAS a Abuja. Shugabannin kasashen kungiyar za su yi nazarin bukatar ka kuma za a dauki mataki."

- A cewar Bola Tinubu, shugaban ECOWAS.

Mali, Burkina Faso da Nijar sun fice daga ECOWAS

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa kasar Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanar da ficewar su daga kungiyar kasashen Afrika ta Yamma.

Kara karanta wannan

Mafarauta sun kashe zakin da ya yi sanadin mutuwar ma'aikacin jami'ar OAU

Jami'an sojojin da ke mulki a kasashen uku sun sanar da hakan ne ta kafar talabijin na kasar Mali, lamarin da ya harzuƙa kungiyar ECOWAS.

Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasashen uku suka fara takun saka da kungiyar wadda ta ƙaƙaba masu takunkumi na horo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel