Murna Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Rabon Tallafin N25,000 Ga 'Yan Najeriya

Murna Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Rabon Tallafin N25,000 Ga 'Yan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta shirya fara rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ciki na tsadar rayuwa da ake fama da ita
  • Ministan tattaƙin arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin za ta raba N25,000 ga iyalai 15m har na tsawon wata uku
  • Gwamnatin za kuma ta raba hatsi ga talakawa domin karya farashin kayan abinci wanda ya yi tashin gwauron zabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya za ta raba Naira 25,000 duk wata ga iyalai miliyan 15 a fadin ƙasar nan a wani mataki na rage wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta.

Tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar da ta gabata, Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur, lamarin da ya kai ga ruɓanya farashin man fetur da tsadar rayuwa yayin da darajar Naira ta yi warwas a ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gamu da sabuwar matsala, ASUU zata sa kafar wando ɗaya da FG kan muhimmin abu 1

FG za ta raba N25,000
FG za ta raba N25,000 duk wata ga iyalai 15m Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Manufofin gwamnati mai ci sun jefa ƴan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya sa mutane da dama ke kokawa wajen samun abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ƙasar nan da dama sun fito kan tituna domin nuna rashin jin dadinsu da salon shugabancin Tinubu.

Wane ƙoƙari FG ke yi don rage wahala?

Da yake jawabi a wata hira ta musamman a gidan talabijin na Channels tv, ministan kuɗi, Wale Edun, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin rage wahalhalun da ake fama da su, musamman ga talakawa da marasa galihu.

"Amma ina ganin muhimmin abin da ya kamata a yi nuni da shi, a wannan lokaci, shi ne, abin da shugaban ƙasa ya mayar da hankali a kai shi ne cika alƙawarin da ya ɗauka, musamman ga talakawa da marasa galihu.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

"An ƙara farashin kayan abinci, kuma ƙarfin saye ya ragu kuma abin da shugaban ƙasar ke magana kai tsaye kenan ta shirin shiga tsakani na biyan Naira 75,000 kai tsaye a cikin watanni uku.
"N25,000 ne a wata ga iyalai miliyan 15 kuma kowane gida kusan mutum biyar ne. Don haka, hakan ya samar da tallafi ga mutane miliyan 75."

Ministan ya kuma sake jaddada shirin Gwamnatin Tarayya na samar da hatsi don taimakawa wajen rage tsadar kayan abinci.

Malamin Addini Ya Shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban limamin cocin Anglican ta Ikwerre a jihar Rivers, ya shawarci Shugaba Tinubu kan halin da ake ciki a ƙasar nan.

Fasto Blessing Enyindah ya buƙaci shugaban ƙasan da ya gaggauta ceto ƴan Najeriya daga halin wahala da suke ciki tun kafin lokaci ya ƙure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel