Tsadar Rayuwa: Babban Malamin Addini Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Shugaba Tinubu

Tsadar Rayuwa: Babban Malamin Addini Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Shugaba Tinubu

  • An yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ceto ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan
  • Limamin cocin Anglican ta Ikwerre, Dr Blessing Enyindah, ya yi wannan kiran a wajen jana'izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu
  • Malamin addinin ya buƙaci shugaban ƙasan da ya gaggauta share hawayen ƴan Najeriya saboda babu lokacin ɓata wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Limamin cocin Anglican ta Ikwerre, a jihar Rivers, Dr Blessing Enyindah, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta.

Ƴan Najeriya da dama dai sun yi ta roƙon gwamnati da ta lalubo hanyoyin magance ƙarin farashin kayan abinci da ake ci gaba da fuskanta a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Murna yayin da aka fadi lokacin kawo karshen 'yan bindiga a jihar Arewa

An ba Shugaba Tinubu shawara
Ana ci gaba da matsin lamba ga Shugaba Tinubu kan tsadar rayuwa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Enyindah, ya yi magana ne a lokacin da yake huɗuba a jana’izar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu a cocin Saint Andrews Cathedral Church Imola, Owo, jihar Ondo a ranar Juma’a, cewar rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wacce shawara ya ba Shugaba Tinubu?

Babban malamin addinin ya buƙaci shugaban ƙasar da ya gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin, rahoton Leadership ya tabbatar.

A kalamansa:

"Bari in yi addu’a a madadin ƴan Najeriya tare da yin kira ga shugaban ƙasa, Sanata Bola Tinubu da ya yi wani abu don rage wahalhalun da ƴan Nijeriya ke fuskanta.
"Muna da fatan zai yi saboda ya yi mana alƙawarin sabunta fata kuma a cewarsa, lokacin sa ne, don haka aka ba shi lokaci da dama a yanzu. Muna jira tare da fata cika alƙawarin sabunta fata.
"Muna roƙonsa da ya yi shi da sauri domin lokaci, wato shekaru huɗu ko takwas ne kamar yadda lamarin ya kasance, gajeru ne kuma lokaci yana tafiya."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kashim Shettima Ya Fadi Abu 1 da Tinubu ke yi wanda zai faranta ran 'yan Najeriya

Akeredolu, wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Disamban 2023, a lokacin da yake jinya a ƙasar Jamus, an yi jana’izar shi a garin Owo a ranar Juma’a, 23 ga watan Fabrairun 2024.

Sheikh Jingir Ya Shawarci Tinubu

A wani labarin kuma,.kun ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya shawarci Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.

Shugaban na ƙungiyar Izalah ɓangaren Jos, ya buƙaci shugaban ƙasan ya dawo da tallafin ne domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke sha sakamakon tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel