El-Rufai Ya Magantu Kan Malamin Musulunci da Ya Nemi a Hallaka Remi Tinubu Kan Wani Dalili

El-Rufai Ya Magantu Kan Malamin Musulunci da Ya Nemi a Hallaka Remi Tinubu Kan Wani Dalili

  • Yayin da ake Allah wadai da kalaman wani malamin addini a jihar Sokoto, Hon. Bello El-Rufai ya yi magana kan batun
  • Dan majalisar da ke wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Dokoki ya ce malamin ya rike neman afuwar da ya yi ba a bukata
  • Bello ya bayyana haka a shafinsa na X a jiya Juma’a 23 ga watan Faburairu kan kalaman malamin da ke jihar Sokoto

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Hon. Muhammad Bello El-Rufai ya yi magana kan malamin da ya ce ya kamata a halllaka matar shugaban kasa, Remi Tinubu.

El-Rufai ya ce ya kamata a kama malamin kuma bai kamata a yi la’akari da neman afuwa da ya yi ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Bello El-Rufai ya yi magana game da kalaman malami kan Remi Tinubu
Bello El-Rufai ya yi Allah wadai da kalaman malamin Musulunci kan Remi Tinubu, Hoto: @B_ELRUFAI/@SenRemiTinubu.
Asali: Twitter

Menene Bello El-Rufai ke cewa?

Dan majalisar da ke wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Dokoki ya ce malamin ya rike neman afuwar da ya yi ba a bukata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello ya bayyana haka a shafinsa na X a jiya Juma’a 23 ga watan Faburairu kan kalaman malamin da ke Sokoto.

Duk da yanzu ya goge wallafawar da ya yi, dan Majalisar ya bukaci jami’an tsaro da su kama malamin tare da hukunta shi.

Martanin da Bello ElRufai ya yi kan kalaman malamin
Bello El-Rufai ya bukaci kama malamin da ya yi kalaman ga Remi Tinubu.
Asali: Twitter

Martaninsa kan kalaman malamin

A cewarsa:

“Ya rike neman afuwar da ya yi, ya kamata a kama shi kuma a hukunta shi nan take ba tare da bata lokaci ba.”

Bello ya fadi haka ne bayan wani mai amfani da kafar X ya wallafa bidiyon malamin ya na neman afuwa.

Wanda ya wallafa bifiyon ya bukaci hukumar DSS da ta kama malamin inda ya ce ya kamata a dawo da dokar sa ido ga malaman addini.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zakzaky yana magana kan harsashi 38 da likitoci suka gano a kwakwalwarsa ya yadu

Shehu Sani ya yi magana kan batun

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da kalaman wani malami da ya bukaci a hallaka matar Tinubu saboda ita Fasto ce.

Sani ya ce caccakar ‘yan siyasa da gwamnati ‘yancin dan kasa ne amma kiran kisan matar shugaban kasa babban kuskure ne kuma ba a bin yarda ba ne.

Wannan na zuwa ne bayan wani malamin addinin Musulunci ya furta cewa ya kamata a hallaka Remi Tinubu saboda Fasto ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel