Tinubu Ya Yi Zancen Mayar Da Tallafi da Soke Karya Naira Saboda Shiga Kuncin Rayuwa

Tinubu Ya Yi Zancen Mayar Da Tallafi da Soke Karya Naira Saboda Shiga Kuncin Rayuwa

  • Bola Ahmed Tinubu ya sake nanata cewa ya fito da tsare-tsarensa ne domin ganin ya bunkasa tattalin arzikin Najeriya
  • Ana kuka da yadda aka janye tsarin tallafin fetur da kuma karya Naira, wasu suna ganin hakan ya jawo wahalar rayuwa
  • Shugaba Bola Tinubu da ya yi zama da tawagar CCA, ya sha alwashin cewa ba zai soke duk manufofin da aka fito da su ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta lashe aman da tayi wajen kokarin kawo gyare-gyare a mulki ba.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban Najeriyan ya tanka masu bada shawarar a sake duba matakan tattalin arzikin da aka dauka.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Bola Tinubu
Tallafi: Bola Tinubu ya hadu da shugabannin CCA a Aso Villa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Cire tallafin fetur da na Dalar Amurka

Kafin a je ko ina, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin fetur, daga baya sai CBN ya daidaita farashin kudin waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin Dala tana tashi a kusan kowace rana sannan rayuwa ta kara kunci, wasu sun bukaci gwamnati ta soke tsare-tsaren da aka kawo.

Tinubu ba zai soke tsare-tsarensa ba

Bola Tinubu ya aika martani ga kungiyoyi irinsu NECA da MAN, ya shaida masu cewa babu ja da baya, sai hakarsa ta cin ma ruwa.

A jawabin da aka samu a shafin Olusegun Dada a X wanda hadimin shugaban kasar ne, Bola Tinubu ya jero amfanin manufofin na sa.

Shugaba Tinubu ya ce za a ga cigaba

Shugaban na Najeriya ya ce gyare-gyaren da ya kawo za su taimaka wajen bunkasa harkar kasuwanci kuma a samu arziki a kasa.

Kara karanta wannan

Bai da wata mafita: Tsohon abokin siyasar Tinubu yayi wa gwamnatin APC kaca-kaca

Tinubu ya bayyana wannan ne a lokacin da yake karbar bakuncin Florizelle Liser ta CCA wanda tayi alkawarin za su taimaka masa.

CCA za ta hada-kai da gwamnatin Tinubu

Kamar yadda bayanai su ka zo mana, shugabannin kungiyar CCA ta nahiyar Afrika sun yi zama da Bola Tinubu a birnin tarayya Abuja.

A wajen wannan zama ne Tinubu ya yabi yadda aka shimfida kilomita 45, 000 na wayoyin yanar gizo daga nahiyar Turai a Akwa Ibom.

Ajuri Ngelale ya ce tun yana gwamnan Legas, Tinubu yake da kyakkyawar alaka da CCA wanda za su bada gudumuwar inganta tattali.

Gwamnatin Tinubu da ASUU

Kungiyar ASUU ta ji babu dadi musamman a lokacin da Muhammadu Buhari yake wa’adinsa na karshe, a yanzu Bola Tinubu ne a mulki.

An ji labarin yadda shugaba Bola Tinubu ya kama hanyar farantawa ASUU, ya biya su albashin watanni hudu kuma zai cire su daga IPPIS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel