Halin Kunci: Yan Najeriya Sun Sako Jarumar Fim a Gaba Kan Kamfen a Zabi Tinubu, Ta Shiga Damuwa

Halin Kunci: Yan Najeriya Sun Sako Jarumar Fim a Gaba Kan Kamfen a Zabi Tinubu, Ta Shiga Damuwa

  • Yayin da mutane ke cikin halin kunci a Najeriya, wasu jarumai da mawaka sun fara shan suka musamman kan zaben Tinubu
  • Jarumar fina-finan Nollywood, Toyin Abraham ta na daga cikin wadanda ke shan suka wanda har ya fara damunta kan zaben Tinubu
  • Jarumar a lokacin kamfen zaben 2023 ta yi ta tallata BolaTinubu don tabbatar da ya yi nasara wanda yanzu ake dana sanin haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Fitacciyar jarumar fina-finai, Toyin Abraham ta shiga tsaka mai wuya kan yin kamfen ga Shugaba Bola Tinubu.

A duk lokacin da jarumar ta wallafa wani abu a kafar sadarwa ta na cin karo da zage-zage da kushe-kushe kan matsayarta a zaben 2023, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Jarumar fim ta shiga halin matsi bayan ta yi kamfe a zabi Tinubu
Jarumar fim, Abraham ta shiga wani irin yanayi kan fatawar a zabi Tinubu. Hoto: Toyin Abraham
Asali: Instagram

Menene mutane ke cewa kan jarumar?

Mafi yawan mutane na yawan wallafa rubutu kamar haka ‘Ubangiji ya miki rahama’ a cikin sashin sharhi nata, cewar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ta ke martani, Abraham ta ce ta na sane da irin halin kunci da ake ciki inda ta ce komai zai zo ya wuce amma tabbas ta na cikin kunci.

A cewarta:

“Ba zai misaltuba, amma ubangiji zai fitar da mu a wannan yanayi, yadda mutane ke saka ni a gaba shi ya fi damuna.”

Martanin mutane kan jarumar

Yayin da wata ke martani kan wani wallafawarta a Istagram, Nkem Diana ta ce:

“Yar Asiwaju, ubangiji zai ziyarce ki kuma ya miki hukunci nan ba da jimawa ba, baki ma fara kuka ba tukun.”

Wani kuma a bangarensa ya mata martani da cewa ta yaudari ‘yan Najeriya wurin saka su zabar shirmen jam’iyya irin APC, cewar Ripples.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Yayin da wani ya kareta da cewa, bai kamata mutane su saka ta a gaba ba saboda babu wanda ta tilasta ya zabi Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan caccakarta da aka yi kan rarraba kayan rage radadi yayin da ake cikin wani hali.

Jarumar fim ta bayyana amfanin saduwa kafin aure

A wani labarin, kun ji cewa jarumar fina-finan Nollywood, ta bayyana amfanin saduwa kafin aure.

Jarumar ta ce ya na da muhimmanci kasan wanda za ku zauna zaman aure don magance matsalolin da ka iya tasowa bayan aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel