Yan ta'adda
Tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe Christopher Inalegwu, yayan kwamishinan labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Benue a yau Litinin.
Mutane da dama sun halaka sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja, sun babbake gidaje da yawa.
Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya sanar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo cewa shi da gwamna Aminu Bello Masari ba su bacci.
'Yan ta'adda da ake zargin mayakan ta'addanci ne na ISWAP wadanda suka kai farmaki kauyen Kautikari da ke karamar hukumar Chibok Borno sun sako 'yan mata hudu.
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da halakar rayuka 11 a yankin kudancin Kaduna a ranar Lahadi, yayin da 'yan bindiga suka babbaka gidaje sama da talatin.
Ran mutum daya ya salwanta a wani farmaki da 'yan fashi da makami suka kai wa tawagar basarake a Abia, Mai Martaba Eze Injiniya Ude, tare da wasu mutum hudu.
Dattijon da yan bindiga suka yi garkuwa da shi a gonarsa da ke garin Faskari, Katsina, Sa’idu Dabo, ya bayyana cewa ya sha jiba a hannunsu kafin a sako shi.
‘Yan bindiga sun kai farmaki wasu anguwanni biyu, Fungan Bako da Kawo da ke karamar hukumar Rafi a Jihar Neja inda suka halaka mutane 2 kuma suka sace wasu.
Shugaba Buhari ya sake umurtan rundunar sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro da su yi maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke yiwa tsaron kasar zagon kasa.
Yan ta'adda
Samu kari