Yadda yan bindiga suka yi mun dukan tsiya kafin a biya kudin fansa, Dattijo

Yadda yan bindiga suka yi mun dukan tsiya kafin a biya kudin fansa, Dattijo

  • Dattijon nan da ya yaye rufin gidansa don ceto yaronsa daga masu garkuwa da mutane ya yi karin haske kan halin da ya shiga a lokacin da aka yi garkuwa da shi
  • Mallam Sa'idu Dabo ya ce yan bindigan su kan jibge su sannan su hana masu sallah a iya zaman da yayi a hannunsu
  • Hakazalika, ya ce su kan basu abinci cokali biyu da safe daga nan kuma sai dare su kara masu wani cokalin

Dattijon da yan bindiga suka yi garkuwa da shi a gonarsa da ke garin Faskari, jihar Katsina, Sa’idu Dabo, ya bayyana halin da ya shiga a hannunsu.

An dai tattaro cewa tsohon ya shafe tsawon kwanaki 11 a hannun maharan kafin suka sako shi bayan an biya kudin fansa N50,000.

Kara karanta wannan

Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA

A wata hira da yayi da jaridar Premium Times Hausa, Dabo ya ce bayan yan bindigan sun yi garkuwa da shi sai suka kai shi sansaninsu inda aka yi masu horo da yunwa tare da hana su yin ibada.

Ya kuma bayyana cewa ba a kashe kowa ba a iya zamansa a hannunsu amma suna shan bugu a hannunsu domin har sai da suka yi masa raunuka sakamakon dukan da suke yi mai.

Yadda yan bindiga suka yi mun dukan tsiya kafin a biya kudin fansa, Dattijo
Yadda yan bindiga suka yi mun dukan tsiya kafin a biya kudin fansa, Dattijo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta nakalto yana cewa:

"Ranar Asabar na je ina kalar dawa a gona, kimanin karfe 2:00 na rana sai ga wadannan mutane suka zo suka dauke ni, sai suka ce na zauna, sai na zauna, suka ce na kwanta, na kwanta, suka ce tashi sai na tashi, sai suka daure hannuwana a bayana sai suka ce mu tafi daba.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

"Da muka je daba, ba sallah, ba cin abinci. Da safe idan aka baka abinci bai fi cokali biyu ba kuma sai da daddare a baka wani. Kuma idan suka zo za ka gansu da bindigogi sun kewaye ku, kuma a gindin icce ake daure mutum.
"Mata sune ake dan sawa ganye a baibaye masu a sa su ciki amma namiji a gindin icce yake harkokinsa."

Kan ko sun taba kashe wani a gabansa, dattijon ya ce:

“A’a basu kashe ba, sai dai bugu, kwarai nima sun buge ni harma da tabo."

Game da yadda suka sake shi, Faskari ya ce:

“Da farko suka ce sai an basu N300,000, ana haka suka yi tsaye kan N300,000, na ce masu ni bani da su, aka dawo N150,000. Toh da na nuna masu ni bani da su sai suka ce ya kenan, sai na ce wa yaro mai aka samu a nan gida, dangi da al’umman Annabi sun hada kudi N50,000. Sai suka bude baki suka ce toh kawo N50,000 din."

Kara karanta wannan

Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON

Daga nan sai yaron nasa ya daura inda yace:

“Sai suka ce na duka ga tsohona nan na gaishe shi, sai na duka gindin wata bashiya sai na gansu. Lokacin da na gansu ma ban gane su ba don duk sun rame sun yi baki sun sha wuya, an daure su da sarka irin ta huda shanu, sai na duka sai ya ganni y ace Ibrahim ne sai na ce eh. Sai yace Allah sarki rayuwa.
“Sai suka ce toh yanzu kai maigida za mu sakeka ka koma gida ka samo N100,000 ka amshi yaronka sai ya ce toh. Amma basu sake shi ba sai da ya kara kwana daya wanshegari Juma’a misalin karfe 10:00 sai suka zo suka dauke shi sai suka sake shi.”

Yadda wani dattijo ya yaye rufin gidansa don ya biya kudin fansar dansa a Katsina

A baya mun kawo cewa wani manomi a Katsina, Saidu Faskari, ya cire rufin gidansa domin ya siyar yayin da yake tattara kudaden da zai biya fansar babban dansa.

Kara karanta wannan

Ustazai: Wankan kamala na amarya da ango a wajen liyafar aurensu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

Karamar hukumar Faskari na daya daga cikin yankunan da ke kan gaba a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa yankin. Yankin na daya daga cikin wurare 13 da Gwamna Bello Masari ya datse layukan sadarwa daga cikin kokarin magance rashin tsaro.

Wani dan jarida daga Faskari, Ibrahim Bawa ya fada ma jaridar Premium Times cewa dattijon bai samu damar hada kudin fansar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel