Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

  • Yan bindiga sun kai farmaki garin Fungan Bako da Kawo da ke karkashin karamar hukumar Rafi a cikin Jihar Neja
  • Sakamakon farmakin, sun halaka mutane 2 sannan sun yi garkuwa da fiye da mutane 100 ciki har da wata mata mai ciki da diyar ta
  • Daga bisani sun saki matar mai ciki bayan ta yi tafiya da kafar ta na tsawon lokaci amma sun wuce da diyar ta mai shekaru 2

Niger - ‘Yan bindiga sun kai farmaki wasu anguwanni biyu, Fungan Bako da Kawo da ke karkashin karamar hukumar Rafi a Jihar Neja inda suka halaka mutane 2 sannan suka sace mutane fiye da 100.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cikin wadanda suka sace har da wata mata mai ciki da yarinyar ta mai shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100
Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Sai dai bayan matar ta sha tafiya a kasa na tsawon lokaci sun sako ta amma sun tsere da diyar ta.

Wata majiya mai karfi a yankin ta ce ‘yan ta’addan sun zo a fiye da babura 30 a ranar Alhamis da misalin karfe 11:00 na dare inda suka ci karen su babu babbaka har safiyar Juma’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce ko wanne babur ya na dauke a kalla maza biyu masu miyagun makamai.

Take a nan suka halaka mutane biyu yayin da suke kokarin tserewa daji, kamar yadda rahoton ya nuna, Vanguard ta ruwaito hakan.

Yanzu haka mutanen da ke zama a kauyakun sun tsere don tseratar da rayuwar su.

Majiyar tace:

“Gaba daya mazauna Tungan Bako da Kawo sun bar kauyakun zuwa garuruwa daban-daban.
“Bayan sa’o’i 24 da faruwar lamarin ‘yan bindigan sun bukaci N70,000,000 a matsayin kudin fansa don sakin wadanda suka sace.

Kara karanta wannan

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

“Sun kira mu inda suka ce suna bukatar kudin fansa N70,000,000 kafin su saki jama’a amma yanzu ba mu da amsar da za mu ba su don ba mu san ta inda za mu fara ba.”

Sai dai an tura jami’an tsaron hadin guiwa yankin don su binciko maharan kuma su ceto wadanda suka sace.

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa sun kai farmaki karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, a wannan karon sun sheke mutum 1 yayin da suka yi garkuwa da sauran mutanen kauyen guda 15, wadanda yawancin su mata ne.

Channels TV ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan kamar yadda aka bada labari sun kai farmaki kauyen Batagari a yankin Maikujeri na karamar hukumar, yayin da suka bayyana a kan babura.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sun iso kauyen ne yayin da suka yi ta harbi a iska dan su jefa firgici a zukatan mazauna kauyen.

Kara karanta wannan

Kotun Italiya ta saka doka kan banɗaki mai ƙara, ta ce hakan shiga hakkin bil’adama ne

Asali: Legit.ng

Online view pixel