Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa gwamnati, masarauta da mutanen jihar Sokoto ta'aziyyar rashin da suka yi sakamakon hare-haren yan bindiga
  • Buhari ya bayar da tabbacin cewa Najeriya za ta yi nasara a yaki da take yi da miyagu
  • Ya kuma jadadda cewa ya ba rundunar sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro umurnin yin maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke yiwa tsaron kasar zagon kasa

Sokoto - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake umurtan rundunar sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro da su yi maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke yiwa kokarin kawo zaman lafiya, tsaro da daidaituwar kasar zagon kasa.

Buhari ya kuma bayar da tabbacin cewa kasar za ta yi nasara a kan miyagun mutane.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook mai taken "Za mu yi nasara a kan miyagun mutane, Shugaba Buhari ya bayar da tabbaci a ziyarar ta'aziyya a Sokoto."

Kara karanta wannan

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsaloli, Buhari ya ba da tabbaci
Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsaloli, Buhari ya ba da tabbaci Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Da yake magana a fadar mai martaba Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar III, shugaban kasar ya ce:

“Na basu umurni cewa kada su kyale kowani dan fashi ko dan ta’adda da ke barazana ga rayuka da dukiyar yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba.”

Buharir, wanda ya mika ta’aziyya ga gwamnati da mutanen Sokoto a kan rashi da suka yi na rayuka da dukiya sakamakon munanan hare-haren yan bindiga da sauran miyagu, ya ba su tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba a kokarinsa na kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar da sauran yankunan kasar.

Shugaban kasar ya rubuta a rijistar baki:

“Ina mika ta’aziyyata ga masarauta, gwamnati da kuma mutanen jihar Sokoto kan kisan rashin imani da yan bindiga da yan fashi suka yi.

Kara karanta wannan

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

“Najeriya za ta yi nasara a yaki da miyagu.”

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da Sultan sun yi godiya ya shugaban kasar a kan tausayawar da ya nuna inda suka bashi tabbacin ci gaba da mara masa baya a wajen samun zaman lafiya da daidaituwar kasar.

Shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin simintin BUA

A gefe guda, mun ji a baya cewa, a ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin simintin BUA mai karfin samar da tan miliyan uku a Sokoto da misalin karfe 12:20 na rana.

Shugaban ya samu rakiyar Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefele; Shugaban rukunin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi'u da shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da sauransu.

Jim kadan bayan kaddamar da kamfanin, shugaban kamfanin, Alhaji AbdulSamad Rabi’u, ya zagaya da shugaban kasar tare da tawagarsa.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Asali: Legit.ng

Online view pixel