Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

  • Rundunar 'yan sanda ta yi ram da wasu 'yan ta'adda a jihar Sokoto, ana zargin yaran Bello Turji ne
  • Daya daga cikinsu, ya amsa cewa yana yiwa Bello jinya, kuma yakan sayar masa da kwaya
  • Sai dai, a bangare guda ya bayyana cewa, an kama shi a baya kuma ya tuba daga barnar da yake yi

Jihar Sokoto - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an kama wani likita da ake zargin ya yi jinyar harbin bindiga ga dan ta'adda Bello Turji a jihar Sokoto.

An kama likitan mai suna Abubakar Kamarawa ne a wani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai kan 'yan ta'addan.

An kama shi ne tare da wasu 'yan ta'addan a wasu ayyuka daban-daban a fadin kananan hukumomi uku na jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu
Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu |. Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kananan hukumomin sun hada da, Illela, Rabah da Goronyo, duk a yankin gabashin Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar ya amince cewa yana jinyar ‘yan bindigar da suka samu raunuka a wani artabu da jami’an tsaro tare da kawo musu kayan buguwa.

Ya fadi dalla-dalla yadda ya yi wa Turji jinya bayan samun raunin harbin bindiga a kai kimanin shekaru uku da suka wuce.

Likitan, wanda ya mallaki kantin magani a Kamarawa, ya ce wani Musa ne ya gabatar da shi ga Kasurgumi Turji.

A cewarsa:

“Musa ya kai ni ga Turji lokacin da aka harbe shi a kai a shekarun baya. Ya kai ni sansaninsa inda na yi masa magani."

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kasance suna zuwa shagonsa domin neman magani da kayan buguwa, ciki har da allurar nan ta Pentaxocine.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

“Amma na tuba tun bayan kama ni da akayi aka hukunta ni kimanin shekaru biyu da suka wuce. A gaskiya, na bar yankin kuma yanzu ina zaune ne a cikin babban birnin jihar."

‘Yan Sanda sun cafke miyagu sama da 50 da ke tare da gawurtaccen ‘Dan bindiga Turji

Aminiya ta fitar da rahoto a yau Litinin, 31 ga watan Junairu 2022, ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kai wani farmaki, sun yi ram da yaran Bello Turji.

Dakarun ‘yan sandan na Najeriya sun yi dace sun damke wadannan ‘yan bindiga ne da suka kai farmaki a garuruwan Goronyo, Rabah da Illela duk a Sokoto.

Mataimakin sufeta na ‘yan sanda, DIG Zaki M. Ahmad ya jagoranci farmakin da aka kai, har aka kama mutane 37 da ake zargin cewa miyagun ‘yan bindiga ne.

An kuma cafko gama-garin mutane 20 da ake tuhuma da laifin alaka da wadannan ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

A wani labarin, gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sanda da ya taso daga Abuja ya yi hatsari a filin tashi da saukar jiragen sama na Bauchi, Hukumar Binciken Hatsari ta bayyana a ranar Alhamis.

Sai dai, ba a sami asarar rai ba, in ji rahoton na AIB.

A cewar sanarwar da The Nation tace ta samo:

“A ranar 26 ga Janairu, 2022, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta sanar da Ofishin Binciken Hatsarin Hatsari, Najeriya game da wani hatsarin da ya rutsa da wani jirgin sama mai lamba Bell 429 mai lamba 5N-MDA mallakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF).

Asali: Legit.ng

Online view pixel