'Yan bindiga sun farmaki jigon APC, sun sace shi tare da wasu mutum hudu

'Yan bindiga sun farmaki jigon APC, sun sace shi tare da wasu mutum hudu

  • 'Yan bindiga sun farmaki jigon jam'iyyar APC yayin da yake tuki a motarsa a hanyar Isan-Iludun da ke jihar Ekiti a yammacin ranar Litinin
  • Maharan da suka boye a daji sun harbi motarsa sannan suka tisa keyarsa da na wani da ke motar tare da shi
  • Hazalika yan bindiga suka yi awon gaba da wasu masu kona gawayi a yayin da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a jihar

Ekiti - Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon Shugaban karamar hukumar Ilemeje da ke jihar Ekiti, Prince Bamgboye Adegoroye da wasu mutane hudu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an yi garkuwa da Adegoroye, wanda ya kasance babban jigon kungiyar kamfen din Tinubu a kudu maso yamma (SWAGA) a Ekiti, tare da wani mutum guda a motarsa a hanyar Isan-Iludun a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

'Yan bindiga sun farmaki jigon APC, sun sace shi tare da wasu mutum hudu
'Yan bindiga sun farmaki jigon APC, sun sace shi tare da wasu mutum hudu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake bayyana hakan ga yan jarida a Ado Ekiti, shugaban karamar hukumar Ifesowapo da ke jihar Ekiti, Mista Kayode Akerele, ya ce an sace su zuwa wani wuri da ba a sani ba da misalin karfe 7:30 na yamma bayan sun dauke su a wannan hanyan.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun ji cewa tsohon shugaban karamar hukumar da wani da ke motar suna tuki a wannan hanyan lokacin da yan bindigar da suka boye a daji suka harbi motarsa.
“Hakan ya sa dole suka tsaya saboda harbin ya samu motarsu kuma a daidai wajen ne aka sace su sannan kuma ba mu ji ko an kira iyalan ba.”

Shugaban karamar hukumar Ero, Mista Akin Alebiosu, ya ce an kuma yi garkuwa da wasu masu kona gawayi uku a kewayen Ikun-Ekiti da misalin karfe 6:30 na yammacin wannan rana.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

Alebiosu ya bayyana cewa shugaban kungiyar masu kona gawayi mai suna Olu, wanda ya kasance dan Ikun-Ekiti da sauran wadanda lamarin ya ritsa da su sun kasance a yankin kogin Ero don harkokin kasuwancinsu lokacin da lamarin ya afku.

Alebiosu da Akerele sun roki kwamishinan yan sandan jihar Ekiti, Mista Babatunde Mobayo, da ya tsaurara matakan tsaro a hanyar yankin Ayade-Idan-Iludun-Ikun da ya fara zama matattarar yan bindiga a baya-bayan nan.

Da aka tuntube shi, kwamandan rundunar Amotekun a Ekiti, Birgediya Janar Joe Akomolafe, ya ce suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don ceto mutanen.

Jihar Neja: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe sojoji 3 da mazauna da yawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun 'yan bindiga sun kashe mutane 11 a garuruwan Neja tsakanin ranakun Lahadi da Litinin, jaridar The Nation ta rahoto.

An tattaro cewa an kashe sojoji uku da 'yan banga hudu da mazauna yankin hudu a hare-haren da suka gudana a kananan hukumomin Mariga da Paikoro na jihar Neja.

Kara karanta wannan

Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2

A Mariga, yan ta’addan sun kai wa sojoji da yan banga harin bazata a garin Kwanan Dutse.

Asali: Legit.ng

Online view pixel