Kaduna: 'Yan ta'adda sun babbaka rayuka 11 yayin da suke bacci, gidaje 30 sun yi kurmus

Kaduna: 'Yan ta'adda sun babbaka rayuka 11 yayin da suke bacci, gidaje 30 sun yi kurmus

  • 'Yan ta'adda sun kai farmaki yankin Atak Mawai da ke kauyen Zaman Dabo da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna
  • A kalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu bayan 'yan ta'addan sun babbake su da ransu yayin da suke tsaka da bacci a ranar Lahadi
  • Ganau ya ce a halin yanzu ba a san yawan wadanda suka rasa rayukansu ba, saboda gida-gida 'yan ta'addan suka dinga bin jama'a

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da halakar rayuka 11 a yankin kudancin Kaduna a ranar Lahadi, yayin da 'yan bindiga suka babbaka gidaje sama da talatin, Vanguard ta ruwaito.

A kalla mutane goma na yankin ne ake zargin sun kone kurmus cikin baccin su yayin da 'yan bindiga suka banka wa yankin Atak Mawai wuta da ke kauyen Zaman Dabo a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Labari da ɗuminsa: Boko Haram sun sako ƴan mata 4 na Chibok da suka sace

Kaduna: 'Yan ta'adda sun babbaka rayuka 11 yayin da suke bacci, gidaje 30 sun yi kurmus
Kaduna: 'Yan ta'adda sun babbaka rayuka 11 yayin da suke bacci, gidaje 30 sun yi kurmus. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC
"An kai mana farmaki da sa'o'in farko na ranar Lahadi, wasu miyagun 'yan ta'adda ne da ba mu sani ba. Sun kashe kusan mutum goma. Maharan sun kone kusan gidaje goma," wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa ya zarga.
"Maharan sun tsinkayi yankin wurin karfe 3 na asuba yayin da mutane ke bacci kuma sun shiga gida-gida inda suka dinga tada hankulan jama'a da mugun aikin su."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya kara da cewa:

"A yanzu da nake muku magana, ba mu san yawan wadanda suka kashe ba balle kuma wadanda suka samu rauni yayin da muka zagaya yankin domin ganin wadanda mummunan lamarin ya ritsa da su."
"Da yawa daga cikin wadanda aka kashe duk konewa suka yi a gidajen su yayin da suke bacci cikin dare," yace.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda a Katsina

"Kayan abincin mutane duk sun lalace, sun kone abubuwan amfanin jama'a. Daga bisani jami'an tsaro sun bayyana domin tabbatar da kwanciyar hankali tare da dakile maharan," yace.

Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta

A wani labari na daban, makiyaya uku aka kashe a sassa daban-daban na Zangon Kataf da karamar hukumar Kauru da ke kudancin jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, reshen kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka, ya sanar da Daily Trust cewa, an tsinta gawar wani makiyayi mai suna Yusuf Mamuda mai shekara goma sha shida a ranar Lahadi a yankin Zaman Dabo da ke masarautar Atyap ta Zangon Kataf, kuma an cire kansa tare da tafiya da shi.

Ya ce an kashe wani mutum tare da dan uwan sa duk a Zangon Kataf din yayin da ya tsaya siyan fetur da babur din sa.

Kara karanta wannan

Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2

Albarka ya ce an kara kashe wani makiyayi mai suna Amadu Surubu yayin da matasa da makamai suka kai farmaki kasuwar Bakin Kogi da ke karamar hukumar Kauru a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel