Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa

Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa

  • Mutum daya ya rasa ran sa yayin da basarake da tawagarsa ke asibiti rai a hannun Allah sakamakon farmakin 'yan fashi da makami
  • An gano cewa, Mai Martaba Injiniya Ude da wasu mutum hudu na kan titin ABSU zuwa Uturu yayin da miyagun suka yi musu kwanton bauna
  • Daya daga cikin mutanen tawagar basaraken mai suna Okehi shi ne ya rasa ransa yayin da basarake ya samu miyagun raunika daga harsashi

Abia - Ran mutum daya ya salwanta a wani farmaki da 'yan fashi da makami suka kai wa tawagar basarake a Abia, Mai Martaba Eze Injiniya Ude, wanda ke tare da wasu mutum hudu.

Mummunan lamarin ya faru ne a kusa da jami'ar jihar Abia, ABSU, da ke kan titin Uturru a karamar hukumar Isuikwuato da ke jihar, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun koma soja bisa aikata 'fashi da makami' a Yobe

Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa
Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

The Nation ta ruwaito cewa, rahotannin da ba a tabbatar da ba sun sanar da cewa wani Okehi ne ya rasa ran sa a take yayin da basaraken ya samu raunika sakamakon ciwon da ya ji da harsashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan fashi da makamin an gano sun yi kwanton bauna ne wurin titin ABSU zuwa Uturu kuma suka bude wuta kan basaraken da tawagarsa.

Edo: 'Yan ta'adda sun sace bakon haure, sun halaka dan sandan da ke kula da shi

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani bakon haure da ke aiki da wata ma’aikata a jihar Edo ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

An samu bayanai akan yadda ‘yan bindigan suka fara da harbe dan sandan da yake kula da shi yayin da yake aikin a kamfanin Hartland da ke kan titin Idegu-Awain a karamar hukumar Etsako da ke Jihar tukunna suka sace shi.

Kara karanta wannan

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

Ganau sun shaida yadda ‘yan bindigan suka bayyana daga daji suka dinga harbe-harbe ko ta ina daga nan suka halaka dan sandan da ke kula da lafiyar shi sannan suka sace shi suka tsere da shi cikin dajin.

Rahotanni sun nuna yadda daga bisani ‘yan sanda suka zo don daukar gawar zuwa ma’adanar gawa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel