Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto sun halaka wasu mutane da ake zargi da ta'addanci har 23
  • Duk a cikin aikin Operation Sahara Storm, sun cafko 'yan bindiga 37 tare da samo shanu da miyagun makamai daga wurinsu
  • 'Yan sandan sun yi aikin kakkabar 'yan ta'addan ne a kananan hukumomi uku na Sokoto inda suka dade suna cin karensu babu babbaka

Sokoto - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta halaka wasu mutum 23 da ake zargin 'yan ta'adda ne, inda suka sake kama yan bindiga guda 37 a kananan hukumomi uku da ke jihar Sokoto.

Yayin zantawa da manema labarai ranar Litinin a Sakkwoto, mataimakin Sifeta Janar, Ahmad Zaki, ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargin da bindiga kirar AK-47 guda 32, makamai masu linzami guda 2, harsasai sama da carbi 1,000 da mugayen makamai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

'Yan sanda sun halaka 23 da ake zargi, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto
'Yan sanda sun halaka 23 da ake zargi, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce an gano hakan ne lokacin da 'yan sanda suke gudanar da aiki na musamman domin yaki da ta'addanci wanda su ka yi wa lakabi da "Operation Sahara Storm".

Channels Tv ta ruwaito cewa, sun gabatar da aikin ne a Illela Goronyo da karamar hukumar Rabah na jihar inda 'yan bindiga da sauran yan ta'adda suke cin karensu babu babbaka.

Kamar yadda Zaki ya bayyana, an sami sama da shanu 150, fiye da kwalaye 40 na miyagun kwayoyi, layu, cajojin batirin sola da sauran abubuwan da ke taimakawa hatsabibai.

DIG ya ce Sifeta Janar na 'yan sanda ne ya bada umarnin gudanar da aikin don yakar ayyukan ta'addanci a yankin arewa-maso-yamma, Channels Tv ta ruwaito.

Daya daga cikin wadanda aka kama, Musa Kamarawa ya bayyanawa manema labarai yadda yake aiki tare da 'yan ta'addan na tsawon shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Labari da ɗuminsa: Boko Haram sun sako ƴan mata 4 na Chibok da suka sace

Ya ce ya amsa N28 miliyan don siyan motar bindigogi daga Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka dasu.

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

A wani labari na daban, ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu anguwanni biyu, Fungan Bako da Kawo da ke karkashin karamar hukumar Rafi a Jihar Neja inda suka halaka mutane 2 sannan suka sace mutane fiye da 100.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cikin wadanda suka sace har da wata mata mai ciki da yarinyar ta mai shekaru biyu.

Sai dai bayan matar ta sha tafiya a kasa na tsawon lokaci sun sako ta amma sun tsere da diyar ta.

Wata majiya mai karfi a yankin ta ce ‘yan ta’addan sun zo a fiye da babura 30 a ranar Alhamis da misalin karfe 11:00 na dare inda suka ci karen su babu babbaka har safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun babbaka rayuka 11 yayin da suke bacci, gidaje 30 sun yi kurmus

Asali: Legit.ng

Online view pixel