Yan ta'adda
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dakile wani mummunan farmaki da wasu da ake zargin mambobin ISWAP ne suka kai caji ofis a birnin Magumeri dake jihar Borno.
Birtaniya ta gargadi mutanenta da ke Amurka cewa akwai yiwuwar kawo harin ta'addanci musamman a wuraren taruwar mutane ko wurin da baki ke taruwa ko tashohi.
An yi wa hakimi yankan rago, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a garin Tunga Rafin da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi a daren Larabar da ta wuce.
Wasu bayin Allah su biyu sun mutu yayin da wani abun fashewa da aka binne a karkashin kasa ya fashe ya kuma tashi da su a Karamar Hukumar Chikun, jihar Kaduna.
‘Yan bindiga sun aukawa kasuwar Gidan Goga a Zamfara, sun shiga budawa jama’a wuta. Wani 'dan kato da gora da yake rike da bindiga ya yi kukan kura, ya kashe su
Matafiya masu tarin yawa da ba a san adadinsu aka yi garkuwa da su yayin da ‘yan ta’adda suka halaka mafarauta 5 a kusa da Garun Gabas dake Rafi -jihar Neja
Za ku ji cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada sanarwar tallafin N300m na karatu ga marayun da suka rasa iyayensu a yakin Boko Haram.
Dakarun sojin Najeriya sun halaka wasu mayakan ISWAP da Boko Haram sakamakon mummunan arangamar da suka yi a yankin Banki dake karamar hukumar Bama a Borno.
Ana tunanin Natasha Uduaghan tana da alaka da wanda ake zargin ya hallaka mutane. Gwamnati Ta Bukaci a Damke ‘Yar Siyasar Adawa Bisa Zargin Kawo Ta’addanci
Yan ta'adda
Samu kari