Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

  • A karshe gwamnatin tarayya ta magantu a kan harin da wasu yan bindiga suka kai gidan gyara hali na Kuje
  • Sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Shuaibu Balgore, ya tabbatar da cewar kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan harin da yake zargin Boko Haram da kaiwa
  • An dai dawo da fursunoni sama da 300 zuwa yanzu kuma wasu na kan hanya kamar yadda FG ta sanar

Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje biyo bayan harin da wasu yan ta’adda suka kai a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.

A yayin wata ziyara da ya kai cibiyar, sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Mista Shuaibu Balgore, ya yi bayanin cewa an dawo da fursunoni sama da guda 300 kuma wasu na kan hanya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Yan bindiga
Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kara da cewar cibiyar na dauke da fursunoni 994 kuma cewa maharan, wadanda yake zaton yan Boko Haramn ne sun farmaki cibiyar don kubutar da abokan harkarsu, rahoton PM News.

Balgore ya kuma bayyana cewa mutum daya ya mutu sannan wasu uku sun jikkata a yayin harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An samu tashe-tashen hankula a tsakanin mazauna yankin gidan yarin Kuje a Abuja a yammacin ranar Talata bayan sun jiyo karar abubuwan fashewa da na harbi daga bangaren cibiyar.

Wani kakakin hukumar gidan gyara hali na Najeriya, AD Umar, ya tabbatar da cewar yan bindiga sun farmaki gidan gyara halin amma an dawo da zaman lafiya bayan hukumomin tsaro sun shiga lamarin.

Umar ya ce:

“Ina son tabbatar da cewar da misalin karfe 2200, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun farmaki cibiyar gyara hali na Kuje a babbar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni sama da 300 sun tsere

“Sai dai kuma, jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro da ke cibiyar sun mayar da martani kuma an dawo da zaman lafiya a wurin kuma an shawo kan lamarin.”

Yanzu-Yanzu: Abba Kyari, Dariye, Nyame sun tsere daga magarkamar Kuje a wani hari

Mun ji cewa da alamu wasu manyan fursunoni a gidan yari na Kuje da ke Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata.

Harin da ya dauki tsawon sa'o'i kadan, an ce jami'an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.

Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel